Mutane Sun ba APC Shawarar Nada Abdullahi Ganduje a Matsayin Shugaban Jam'iyya

Mutane Sun ba APC Shawarar Nada Abdullahi Ganduje a Matsayin Shugaban Jam'iyya

  • Ganin a yanzu jam’iyyar APC ba ta da cikakken shugaba, an ayyana sunan wanda ya dace da kujerar
  • Wasu sun ce a duk ‘ya ‘yan APC babu wanda ya dace ya jagoranci NWC irin Abdullahi Umar Ganduje
  • Zuwa yanzu babu inda Ganduje ya nuna yana sha’awar ya canji Abdullahi Adamu da ya yi murabus

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Wasu sun fara yin kira ga jam’iyyar APC mai mulki ta nada Abdullahi Umar Ganduje ya zama sabon shugaba na kasa.

Legit.ng Hausa ta bibiyi shafukan sada zumunta, ta gano akwai masu wannan ra’ayi.

Wadanda su ke ganin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya dace ya maye gurbin Abdullahi Adamu, sun yaba da yadda yake kaunar APC.

Abdullahi Ganduje
Abdullahi Ganduje yana cikin manyan APC Hoto: Abubakar Aminu Ibrahim
Asali: Facebook

Gudumuwar Abdullahi Ganduje a APC

Tsohon Gwamnan na jihar Kano ya taka rawar gani sosai wajen ganin Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban Najeriya a Mayu.

Kara karanta wannan

Kura-Kurai, Katobara da Cikas 7 da Abdullahi Adamu Ya Samu a Kujerar Shugabancin APC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Watakila irin kwazon Abdullahi Ganduje a zaben bana ko kuwa gatse da wasa ya jawo aka ji Sanusi Umar Sadiq yana wannan kira.

Da yake magana a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, Lauyan ya ce kyau shugabancin jam’iyyar APC ya fada hannun Ganduje.

A ba Abdullahi Ganduje kawai

"Kano fa gaskiya ana yi ma na kwange. Ai ta cewa mu ne cibiyar siyasa amma dan Kano bai taba shugabancin jam'iyya mai mulki ba.
Yanzu dai gaskiya a bawa Ganduje shugabancin APC."

-Sanusi Umar Sadiq

Sabiu Zaranda wanda ya bayyana kan shi a matsayin ‘dan siyasa kuma mai neman ilmi, yana cikin wadanda su ka fara wannan magana.

Mutumin Bauchin yana ganin tsohon Gwamnan Kano zai dace da shugabantar jam’iyya tun da Abdullahi Adamu ya bar kujerarsa.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Shugaban APC Ya Hakura da Rikon Jam’iyya, Ya Sauka Daga Kujerarsa

"Da ni ne Asiwaju, zan nada Ganduje ya zama sabon shugaban APC na kasa."

- Sabiu Zaranda

Amma wani mai bibiyarsa a Twitter, ya ba shi amsa yana cewa:

Kash! Hakkin Arewa ta tsakiya ne.”

Ko da ba shugaban kasa yake da ikon nada shugabannin jam’iyya ba, da aka nemi jin dalilin Zaranda, sai ya bada amsa da biyayyar Ganduje.

Arewa ta yamma ko Arewa ta tsakiya?

Ana haka ne sai mu ka ji tsohon Gwamnan Filato, Simon Lalong ya ziyarci Sakataren gwamnatin tarayya na kasa, Sanata George Akume a Abuja.

Nan take wasu su ka fara maganar ko shugaban kwamitin yakin neman zaben na Tinubu a 2023 ya fara hangen yadda zai gaji kujerar a NWC.

“Ina fatan Ganduje zai zama sabon shugaban jam’iyyar APC. Ina so ‘yan jam’iyyarsa su ji dadin shi kamar yadda mutanen Kano su ka ji.”

- Inji Aliyu Dahiru Aliyu

Wanene sabon shugaban APC?

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Gwamnan Legas da Wani Gwamnan Arewa a Villa

Za a ji tarihin rayuwa da siyasar ‘dan tsohon Gwamnan tsohuwar Arewa da zai jagoranci APC.

Kyari ya karbi NWC

An samu labari Abubakar Kyari wanda ya yi Kwamishina sau biyar, kuma sau 4 ana rantsar da shi a Majalisar tarayya ya canji Abdullahi Adamu.

Sabon shugaban APC na kasa, Sanata Kyari yana matukar girmama Kashim Shettima wanda yanzu shi ne mataimakin shugaban Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel