Shugaba Tinubu Ya Gana da Jonathan da Wasu Gwamnoni a Aso Villa

Shugaba Tinubu Ya Gana da Jonathan da Wasu Gwamnoni a Aso Villa

  • Tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya gana da shugaba Bola Ahmed Tinubu a Aso Villa da ke Abuja ranar Talata
  • Wasu jiga-jigan gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki da suka haɗa da Hope Uzodinma na Imo da Abdulrahman na Kwara sun halarci taron
  • Jonathan ya bayyana cewa sun tattauna batutuwan da suka shafi nahiyar Afirka da kuma yammacin Afirka da shugaba Tinubu

FCT Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da tsohon shugaban kasa, Dakta Goodluck Jonathan a fadar Aso Villa da ke birnin tarayya Abuja.

Haka nan kuma gwamnonin da suka ƙunshi, Hope Uzodimma na Imo, Dapo Abiodun na Ogun da AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara sun halarci ganawar shugabannin 2.

Hotunan ganawar Jonathan da shugaba Tinubu a Villa.
Shugaba Tinubu Ya Gana da Jonathan da Wasu Gwamnoni a Aso Villa Hoto: @leadership
Asali: Twitter

Channels tv ta rahoto cewa har yanzun ba a bayyana makasudin wannan zama na Tinubu da Jonathan ba ranar Talata, 18 ga watan Yuli, 2023.

Kara karanta wannan

Tsagerun 'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Mutane Wuta a Gargruwa 2, Sun Halaka Mutane da Yawa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wannan ziyara da Jonathan ya kai fadar shugaban ƙasa ta zo ne wata ɗaya tal da yan kwanaki bayan ziyarar da ya kai wa Tinubu ranar 13 ga watan Yuni, 2023, Leadership ta ruwaito.

Wane batutun suka tattauna a lokacin wannan zama?

Jonathan, shugaban tawagar shiga tsakani na ƙungiyar ECOWAS a ƙasar Mali, ya bayyana cewa ganawarsa da shugaban ƙasa ta maida hankali kan batutuwan da suka shafi nahiyar Afirka.

Da yake zantawa da manema labaran gidan gwamnati yayin da zai bar fadar shugaban ƙasa, Jonathan ya ce:

"Na zo nan ne domin na yi wa shugaban ƙasa bayani kan abubuwan da suka shafi nahiyar mu ta Afirka. Ni ne mai shiga tsakanin na ECOWAS a ƙasar Mali kuma ni ne shugaban ƙungiyar dattawan nahiyar Afirka ta yamma."

Kara karanta wannan

Gwamnoni 6 da Shugabannin Ibo Zasu Gana da Shugaba Tinubu Kan Muhimmin Abu 1 Rak, Bayanai Sun Fito

"Saboda haka akwai wasu batutuwa da suka shafi nahiyar mu da kuma wani ɓangaren nahiyar nan da na tattauna shugabanni daban-daban."

Layin Mai Ya Dawo a Abuja da Kano Bayan Kara Farashin Lita Zuwa N620

A wani labarin na daban kuma kun ji cewa Sakamakon tsadar litar man fetur da safiyar Talata, layin shan mai ya dawo a wasu sassan birnin Abuja da Kano.

A gidan man AA Rano da ke Anguwar Utako Abuja, motoci sun jera layi mai tsawo a ciki da wajen harabar gidan man suna jiran sayen Fetur a farashi mai rahusa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel