Siyasar Najeriya
Majalisar dokokin jihar Bauchi ta zabi sabon kakakin majalisa da mataimakinsa bayan kotin daukaka kara ta soke zaben tsohon kakakin majalisar da mataimakinsa.
Shugaban majalisar dokokin jihar Ondo, Olamide Oladiji, ya yai bayanin shawarwarin da aka yanke yayin zaman sulhu da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Jam'iyyar Labour Party (LP) ta zargi kotun koli da kasa yanke hukunci a karar da Peter Obi ya daukaka. Jam'iyyar ta bayyana hakan a matsayin abun takaici.
Kungiyar Progressive League of Youth Voters (PLYV) ta bayyana cewa akwai wani shiri da ake yi na tayar da hargitsi a garin Kano a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba.
Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a birnin tarayya ta yanke hukunci kan ƙarar da ɗan takarar NNPP ya shigar kan nasarar Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba.
Masu zanga-zanga sun dira a hedikwatar jam'iyyar PDP ta kasa kan kiran a kori shugaban jam'iyyar na kasa inda suka bayyana rawar da ya taka a rikicin Wike da Fubara.
Hatsaniya kan batun shugabancin majalisar dokokin jihar Bauchi ta ƙaru bayan kotun ɗaukaka kara ta tuge shugaban majalisar da mataimakinsa kwanan nan.
Jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya yi watsi da raɗe-raɗin da ke yawo cewa Nyesom Wike ne ke daukar nauyin takarar Philip Shaibu a zaben gwamnan Edo.
Jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Bode George, a martanin da ya yi kan tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya ce akwai kuskure alkalai suɓsoke zabe.
Siyasar Najeriya
Samu kari