Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Wasu Ayyuka 2 Da Buhari Ya Fara

Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Wasu Ayyuka 2 Da Buhari Ya Fara

  • Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta bada umurnin dakatar da aikin samar da jiragen sama na kasa da mallakawa kamfanoni filayen jiragen sama
  • Festus Keyamo, Ministan Sufurin Sama da Bunƙasa Harkokin Samaniya, ya bayyana cewa an dakatar da ayyukan har zuwa wani lokaci nan gaba
  • Gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu ne ta bada umurnin sallamar da kamfanin jirgin saman na kasa da filayen jiragen kimanin mako daya kafin karewar wa'adinta

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta hannun Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bada umurnin dakatar da sallama filin tashin jiragen sama da kamfanin jirgin sama na kasa.

A cewar Daily Trust, sallama filin tashin jiragen saman da jirgin sama na kasa na cikin manyan ayyukan da tsohuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi a bangaren sufurin jiragen sama.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sake Ware Biliyoyin Kudade Don Sake Gina Arewa, Ya Bayyana Dalili

Tinubu ya dakatar da wasu muhimman ayuka da Buhari ya yi
Tinubu ya dakatar da aikin kamfanin jirgin sama na kasa da wani abu 1 da Buhari ya fara. Hoto: Bola Tinubu, Festus Keyamo, Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma, Keyamo, yayin wata ziyara da ya kai filin Tashi da Saukan Jirage Na Murtala Mohammed (MMIA) da ke Legas a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta, ya ce a dakatar da ayyukan har zuwa wani lokaci nan gaba.

Yadda Buhari ya bada umurnin ayyukan filayen jiragen sama kimanin mako daya kafin karewar wa'adinsa

Idan za a iya tunawa an amince da yin ayyukan ne a kusan karshen wa'adin gwamnatin Shugaba Buhari, kuma hakan ya janyo cece-kuce tsakanin masu ruwa da tsaki.

Gwamnatin Tarayyar ta sanar da sallamar da filin tashin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja da Murtala Mohammed da ke Legas (MMIA) kimanin mako guda kafin karewar wa'adin gwamnatin Shugaba Buhari.

Keyamo ya umurci a dakatar da aikin Buhari kimanin makonni 2 bayan Tinubu ya nada shi

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu, Keyamo, Ya Bada Umurnin Rushe Filin Jiragen Sama Na Legas, Ya Bada Dalili

James Odaudu, mataimaki na musamman ga tsohon Ministan Sufuri, Hadi Sirika na wancan lokacin, ya bayyana amincewa da sallamar da su a taron FEC.

Tsohon ministan ya bayyana cewa kamfanin 'Corporation American Airport Consortium ne wanda za a sallamarwa kadarorin, ya kunshi Corporation American Airports, Mota Engil Africa, and Mota Engil Nigeria.

An rantsar da Keyamo a matsayin minista a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, lokacin da Shugaba Tinubu ya kaddamar da ministocinsa 45. Shugaba Tinubu ya tura sunayen mutane 48 ga Majalisar Dattawa domin tantancewa amma uku cikinsu ba a tantance su ba.

Ministan ya yi bayani a shafinsa na Twitter:

"Ba a yanke hukuncin karshe ba kan batun sallamar da jirgin saman kasa da filayen jiragen sama. An dakatar da abin ne don tantance lamarin tare da warware korafe-korafen saboda amfanin yan Najeriya kuma an yi wa Shugaban Kasa bayani."

Ga rubutun da ya yi a kasa:

Kara karanta wannan

Jerin Jiga-Jigan PDP Da Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Bai Mukami

Keyamo Ya Bada Umurnin Rushe Filin Jirgin Sama Na Legas

Ministan Sufurin Sama da Bunƙasa Harkokin Samaniya, Festus Keyamo, ya bada umurnin rushe wuraren ajiye jiragen sama na EAN da Dominion a filin tashin jiragen sama na Murtala Mohammed na Biyu (MMIA2) da ke Legas.

Kamar yadda Daily Independent ta rahoto, Keyamo ya bada umurnin hakan ne domin aikin fadada filin jirgin saman da za a yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel