Har Yanzu Rabiu Kwankwaso Na Nan a Jam'iyyar NNPP, In Ji Robert

Har Yanzu Rabiu Kwankwaso Na Nan a Jam'iyyar NNPP, In Ji Robert

  • Mai baiwa NNPP shawara kan harkokin shari'a ya fayyace tanadin doka kan batun dakatar da jagoran jam'iyyar, Rabiu Kwankwaso
  • Mista Robert ya ce BoT bai da hurumin dakatarwa ko korar kowane mamba, bisa haka tsohon gwamnan na nan daram a NNPP
  • A cewarsa masu ruwa da tsakin jam'iyya daga jihohi 36 da Abuja sun zauna sun kaɗa ƙuri'ar kwarin guiwa kan Kwankwaso

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Mai bada shawara kan harkokin shari'a na jam'iyyar NNPP ta ƙasa, Robert Hon, ya jaddada cewa kwamitin amintattu (BoT) bai da ƙarfin ikon dakatar da Rabiu Kwankwaso.

Ya yi bayanin cewa kundin tsarin mulki bai bai wa BoT hurumin dakatar da ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar NNPP, Kwankwaso ba, kamar yadda Punch ta rahoto.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.
Har Yanzu Rabiu Kwankwaso Na Nan a Jam'iyyar NNPP, Robert Hoto: KwankwasoRM
Asali: Twitter

A cewarsa, kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) na NNPP ne kaɗai doka ta bai wa damar ɗaukar matakin dakatarwa kan Kwankwaso kuma shi kansa sai an cika sharuɗɗa.

Kara karanta wannan

Ahaf: Wike Ya Sake Takalar Fada Tsakaninsa Da Atiku, PDP Ya Kalubalancesu Abu 1

Bisa haka, Mista Robert ya ayyana batun dakatarwan da aka yi wa Kwankwaso da tunanin kwamitin BoT wanda ba bu shi saboda tuni aka rushe shi baki ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa ya ce:

"Tun tuni kuma har zuwa yau Kwankwaso cikakken mamba ne na jam'iyyar NNPP, duk wani ɓangare da ya yi ikirarin dakatar da shi to ya saɓa doka."
"Domin BoT wani ɓangare ne kawai da ake neman shawarinsa amma ba su da hurumin doka na dakatar da kowane mamba."

Wane hali Kwankwaso ke ciki a NNPP?

Ya ƙara da cewa tuni jam'iyya ta gudanar da taron gaggawa a birnin tarayya Abuja, inda daga ƙarshe masu ruwa da tsakin NNPP daga kafatanin jihohi suka kaɗa kuri'ar kwarin guiwa kan Kwankwaso.

A rahoton Business Day, Jigon ya ci gaba da cewa:

Kara karanta wannan

Uwar Jam’iyya Ta Fadi Matsayin Rabiu Kwankwaso a NNPP Ana Tsakiyar Rikici

"Kwamitin amintattu masu bada shawari ne kawai amma ba su da iko a doka su dakatar ko korar wani ɗan jam'iyya, NEC ne kaɗai ke da karfin ikon kora ko dakatarwa."

Ya ƙara da bayanin cewa shugabannin NNPP daga jihohi 36 da Abuja sun zauna kuma sun ƙara tabbatar da Kwankwaso na nan daram a jam'iyya, inda suka kaɗa kuri'ar amincewa da shi.

Shugaba Tinubu Na Ke Yi Wa Aiki Ba Jam'iyyar APC Ba, Nyesom Wike

A wani rahoton kuma Ministan Abuja kuma babban jigon PDP ya fayyace gaskiya kan zargin yana yi wa jam'iyyar APC aiki.

Ya kuma bayyana cewa ba bu wanda ya biyo shi bashin neman tafiya saboda ya mara wa shugaba Tinubu baya a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel