Gwamnan Jigawa Ya Ayyana Shirin Samar da Miloniyoyi 15 Cikin Shekara 4

Gwamnan Jigawa Ya Ayyana Shirin Samar da Miloniyoyi 15 Cikin Shekara 4

  • Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya bayyana shirinsa na samar da Attajiran masu kuɗi 150 a zangon mulkinsa na farko
  • Namadi ya sanar da haka ne a wurin taron raba tallafin dogaro da kai ga mata 1,000 wanda ma'aikatar mata ta jihar ta shirya ranar Alhamis
  • Ya ce gwamnatinsa ta gano basirar da Allah ya baiwa mutanen jihar kuma ta shirya buɗe musu hanyoyin wadata

Jigawa state - Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sanar da wani sabon shiri na inganta rayuwar al’ummar jihar da ke Arewa maso Yamma, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

A wani abin da ya kira da bunkasa tattalin arziki da rage zaman kashe wando, Gwamna Namadi, ya kaddamar da wani shiri na samar da attajirai 150 a wa’adinsa na farko a ofis.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sake Ware Biliyoyin Kudade Don Sake Gina Arewa, Ya Bayyana Dalili

Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi.
Gwamnan Jigawa Ya Ayyana Shirin Samar da Miloniyoyi 15 Cikin Shekara 4 Hoto: dailytrust
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wurin raba tallafin dogaro da kai ga mata 1,000 wanda ma'aikatar kula da harkokin mata ta jihar Jigawa ta shirya da haɗin guiwar hukumar matasa.

Yadda zamu samar da Attajirai 150 - Namadi

Da yake jawabi a wurin taron ranar Alhamis, gwamna Namadi na jam'iyyar APC ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wannan rana ce mai muhimmanci gare mu a jihar Jigawa yayin da muka kudiri aniyar kawo sauyi da ci gaba ga al'umma. Gwamnatinmu na gano basirar jama'ar ta kuma mun shirya buɗe musu hanyoyin samun arziƙi."
“Akwai babban wannan da zai zo nan gaba, kuma da yardar Allah daga nan zuwa shekaru hudu masu zuwa, za mu tabbatar da samar da mutane 150 masu dogaro da kai da za a kira masu kudi a jihar nan."

Kara karanta wannan

Mutane Sun Gaji: An Bayyana Gwamnan APC Da Ke Dab Da Rasa Kujerarsa a Hannun PDP

Daga ƙarshe, Gwamna Namadi ya buƙaci waɗanda suka ci gajiyar shirin ba da tallafin da su yi amfani da abinda suka samu ta hanyar da ta dace kana su gina wa kansu gobe mai kyau.

Bayan haka gwamnan ya yi kira da kowa ya tashi tsaye ya yi aiki tukuru domin dogaro da kansa.

Shugaba Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri da Tsohon Gwamnan Zamfara Yari a Villa

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawar sirri da tsohon shugaban gwamnonin Najeriya, Sanata Abdul'aziz Yari a Aso Villa.

Tsohon gwamnan Zamfara ya ce shugaba Tinubu ba shi da dalilin yin korafi saboda shi ya nemi a zabe shi a matsayin shugaban kasa,

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262