Siyasar Najeriya
Gwamnatin tarayya ta gurfanar da mawallafin shafin yanar gizo wanda ya yi ikirarin tsohon ministan Buhari ne ya rubuta hukuncin kotun zaɓe a karar LP da PDP.
Gwamna Babagana Umaru Zulum na jihar Borno ya amince da naɗin sababbin hadimai 168 da mambobin majalisun gudanarwa na hukumomin gwamnatin jiharsa.
Reno Omokri ya shawarci dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi kgan yadda zai shawo kan Musulmai su zabe shi a 2027 tare da manta abin da ya yi.
Gwamnan Kano ya bayyana kudin da yake kashewa wajen ciyar da Kanawa a cikin watan Ramadana yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan adadin kudin na bana.
An nemi gwamnan Kano ya ba bahasin yadda ya kashe wasu kudade da ake ganin an ware su ne domin ya ciyar da 'yan jihar a cikin watan Ramadanan bana.
An bayyana jihohin Najeriya da suka fi shan tsadar man fetur a Najeriya, duba da yadda farashin ya tashi a gidajen mai a cikin watan da ya gabata.
Jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta yi wa shugaban jam'iyyar APC na kasa martani kan kalamansa na cewa jihar Anambra za ta koma hannun APC.
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya ziyarci dakataccen sanatan Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi, a gidansa da ke birnin tarayya Abuja.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma, Mohammed Idris, ya kai ziyarar kwanaki biyu jihar Kano kuma ya gana da mai girma gwamna, Abba Kabir Yusuf.
Siyasar Najeriya
Samu kari