An Kawo Wata Dabarar Tsige Gwamnan PDP, Magoya Bayan Minista Ba Su Hakura Ba

An Kawo Wata Dabarar Tsige Gwamnan PDP, Magoya Bayan Minista Ba Su Hakura Ba

  • Sabanin Gwamna Siminalayi Fubara da uban gidansa ya raba kan ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a jihar Ribas
  • Mutanen da su ke tare da Nyesom Wike har gobe, sun cigaba da kokarin ganin an yi tsige Gwamnan Ribas
  • Wasu da ke shiga duk inda tsohon Gwamnan ya burma sun soma juya-baya, ba su da niyyar barin Fubara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Rivers - Mai girma Siminalayi Fubara ya jaddada cewa ba zai sallama mulkin da mutanen jihar Ribas su ka damka masa ba.

Vanguard ta ce Gwamnan na Ribas ya yi wannan bayani a wajen wani taron Sarakunan gargajiya da aka yi a garin Fatakwal.

Wike da Fubara
Nyesom Wike da Gwamnan Ribas Hoto: Nyesom Wike, Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

Sakon Simi Fubara ga Nyesom Wike

Gwamna Siminalayi Fubara wanda yake rigima da magajinsa kuma Ministan harkon Abuja, Nyesom Wike ya aika masa sako.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC zai yi murabus daga kan mulki saboda rashin lafiya? Gaskiya ta bayyana da dalilai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fubara ya ce jihar Ribas gadon kowa da kowa ne a karkashin jagorancinsa, ya ce zai kare martabar gwamnati idan yana kan mulki.

A jawabinsa, The Cable ta ce gwamnan ya nuna zai tabbatar da tsaro da zaman lafiya, taimakawa matasa da mutanen karkara a Ribas.

Akwai maganar tsige Gwamnan Ribas?

Duk da kokarin da Bola Tinubu ya yi domin shawo kan rikicin, har yanzu akwai rashin jituwa tsakanin manyan ‘yan siyasan.

Tribune a rahoton da ta fitar a ranar Lahadi, ta ce wadanda su ke tare da Nyesom Wike sun dage domin a tsige gwamnan Ribas.

Kishin-kishin ya ce magoyan bayan sun fitar da tsare-tsaren da ake bukata domin a tuntube mai girma Fubara a majalisar dokoki.

Masu wannan shiri sun lalabi wata kungiyar Neja-Delta da ke kokarin ba gwamnan kariya domin ganin sun ci ma manufar ta su.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna Sani ya caccaki kalaman DHQ kan dalilin jefa bam a taron Musulmai, ya nemi abu 1

Masoyin Wike ya kauce hanya

Chris Ezihuo wanda kowa ya san shi a dandalin X wajen goyon bayan ministan harkokin Abuja ya ja baya a tafiyar Nyesom Wike.

Mista Chris Ezihuo ya ce lokacin Wike yana gwamna, ya nuna masu dole a bi gwamna, yanzu kuma yana yakar magajin shi.

Duk yadda alakarsu take da tsohon gwamna, matashin ya ce ba za su raba kafa wajen goyon bayan da su ke yi wa Simi Fubara ba.

Wike ya ce Fubara ya kona Majalisar Ribas

Ana da labari Nyesom Wike ya yi bayani a game da rikicinsa da Simi Fubara wanda ya zargi Gwamnan Ribas da kona majalisar jiha.

Ministan na Abuja ya yi kokarin wanke kan shi daga hannu wajen tsige gwamnan, yake cewa ua kawo siyasar kabilanci a kan mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel