Jam'iyyar Kwankwaso Ta Fara Shirin Haɗa Karfi da Atiku da Wasu Jam'iyyu? Gaskiya Ta Yi Halinta

Jam'iyyar Kwankwaso Ta Fara Shirin Haɗa Karfi da Atiku da Wasu Jam'iyyu? Gaskiya Ta Yi Halinta

  • Jam'iyyar NNPP ta musanta rahoton da ke yawo cewa ta haɗa maja da jam'iyyar PDP da wasu domin tunkarar 2027
  • Muƙaddashin shugaban NNPP na ƙasa, Abba Ali, ya bayyana cewa rahoton haɗa maja ba gaskiya bane
  • Ya buƙaci yan Najeriya da sauran kasashen duniya su yi watsi da wannan labarin na haɗa kai ko ƙawance da NNPP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya nesanta kansa da shiga tattaunawar haɗa maja da wasu jam'iyyun adawa.

NNPP ta musanta haɗa maja da PDP.
Jam'iyyarmu ba ta shiga wata tattaunawar haɗa maja ba, NNPP ta magantu Hoto: NNPP
Asali: UGC

Jam'iyyar NNPP ta ƙasa ta bayyana haka ne a wata sanarwa da muƙaddashin shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abba Ali, ya fitar a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Bayan shan kashi a zaben gwamnan Kogi, Dino Melaye ya bayyana babban darasin da ya koya

NNPP ta bayyana gaskiya kan batun maja

Ya ce NNPP ba ta daga cikin mambobin gamayyar jam'iyyun da suka cure wuri ɗaya mai sunan, 'Coalition of Concerned Political Parties', kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A rahoton Tribune Online, sanarwan ta ce:

"An jawo hankalin shugabancin jam’iyya kan wasu rahotannin da jaridu suka wallafa cewa an kafa gamayyar jam'iyyu kuma ta ƙunshi NNPP da wasu jam’iyyun siyasa."
"Muna mai farin cikin sanar da cewa babu wani abu makamancin haka. Rahoton wanda ya watsu ranar Jumu'a, 8 ga watan Satumba, 2023 ya nuna cewa NNPP, PDP da wasu jam'iyyu sun haɗa maja."
"NNPP na amfani da wannan dama wajen ƙara jaddada cewa wannan rahoton ƙarya ne kuma bai ma yi kama da gaskiya ba."

Ali ya ƙara da cewa tun bayan zaben 2023, babu wani mamban NNPP da ya zauna da wata jam'iyya, tawaga ko ɗaiɗaiku da nufin tattaunawar haɗa maja.

Kara karanta wannan

Tsige Abba: Magoya bayan Kwankwaso sun shirya gagarumin abu 1 a kotun koli, NNPP ta yi bayani

Ya bukaci ‘yan Najeriya da sauran kasashen duniya da su yi watsi da duk wani labari na NNPP ta hada kai da kulla ƙawance da wata jam’iyya ko jam’iyyu.

Wani jigon NNPP a Kano, Said Abdullahi, ya shaida wa Legit Hausa cewa dama ba su goyon bayan haɗa maja don tarar ma jam'iyya mai mulki.

Ya ce:

"Lokacin da na samu labarin wai za a haɗa maja gaskiya banji daɗi ba, saboda ni bana goyon baya, na tuntubi wasu shugabannin mu a Kano suka ce ba su da labari."
"Amma yanzu na ji daɗi gaskiya kowace jam'iyya ta shirya kawai. A matsayin sabuwar jam'iyya, muna ganin kokarin NNPP a 2023 ya nuna nan gaba zamu bada mamaki."

Kujerun Ciyamomi 31 Sun Fara Tangal-Tangal a Akwa Ibom

A wani rahoton na daban Gwamna Umo Eno ya rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi 31 da ke faɗin jihar Akwa Ibom ranar Alhamis.

Da yake jawabi a wurin bikin rantsuwar kama aiki, Gwamnan ya ce zai kori duk wanda ya ƙauracewa zama a yankinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262