Jam'iyyar LP Ta Fice Daga Shirin Maja da PDP, NNPP? Gaskiya Ta Bayyana

Jam'iyyar LP Ta Fice Daga Shirin Maja da PDP, NNPP? Gaskiya Ta Bayyana

  • Jam'iyyar Labour Party (LP) ta yi magana kan yin ƙawance da jam'iyyun adawa domin kawar da APC a kan madafun iko
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa tana cikin ƙawancen tsundum domin ƙarfafa dimokiraɗiyya a ƙasar nan
  • Ta bayyana cewa ba ta fice daga ƙawancen ba duk da ba ta halarci taron farko ba kan fara zama domin ƙulla ƙawancen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugabancin jam'iyyar Labour ya tabbatar da cewa suna cikin sabon ƙawancen jam'iyyun siyasa da aka ƙaddamar a wannan makon.

A ranar Larabar da ta gabata ne wata ƙungiya ta jam'iyyun adawa guda bakwai suka kafa wani sabon ƙawance a wani yunƙuri na ƙarfafa dimokradiyya a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Kogi: Dan takarar APM ya kai karar Ododo kotu? Gaskiya ta bayyyana

LP ta musanta ficewa daga kawancen kayar da Tinubu
Jam'iyyun adawa na shirya kawance domin kayar da Tinubu Hoto: Mr. Peter Obi, Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Twitter

Ƙungiyar mai taken Coalition of Concerned Political Parties an kafata ne a Abuja a taron da shugabannin jam’iyyun siyasa suka halarta a sakatariyar jam’iyyar Social Democratic Party ta ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, sunan jam'iyyar Labour, wata babbar jam'iyyar adawa, ya ɓace a cikin jerin mambobin ƙungiyar.

Gamayyar ta ƙunshi jam’iyyun Peoples Democratic Party, African Democratic Congress, Social Democratic Party, Peoples Allied Movement, New Nigeria Peoples Party, Young Progressives Party, da Zenith Labour Party.

Lokacin da aka tuntuɓi shugabannin LP sun musanta ficewa daga cikin ƙawancen.

LP na nan daram a maja

A wata zantawa ta musamman ta wayar tarho da jaridar The Punch, Sakataren jam’iyyar na ƙasa Umar Farouk ya bayyana cewa an sanar da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar LP bisa ga yadda aka kafa ƙungiyar.

A kalamansa:

"Su (gamayyar jam'iyyun) sun rubuto kuma sun sanar da mu. Hasali ma, mun fitar da sunayen mutanen da za su wakilci jam’iyyar a wannan zama na jiya ranar Alhamis. Abin takaici, waɗanda ya kamata su kasance a wurin ba su je ba. Amma muna tare da su. LP tana cikin wannan ƙawancen."

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya bayyana gaskiya kan shirin haɗa maja da Kwankwaso da wasu jam'iyyu 6

Da yake bayyana ra’ayinsa, babban mai magana da yawun jam’iyyar LP, Yunusa Tanko, ya bayyana cewa, manufar ƙungiyar ita ce kare manufofin dimokuradiyya da tabbatar da cewa ƙasar ba ta faɗa cikin tsarin jam’iyya ɗaya ba.

"Jam’iyyar LP ta yi magana ne da jam’iyyun PDP, NNPP da ƙoƙarin ganin yadda za mu yi magana a matsayinmu na baki ɗaya domin ceto dimokuraɗiyya wanda dukkanmu masu ruwa da tsaki ne a cikinta." A cewarsa.

Atiku Ya Yi Magana Kan Maja

A wani labarin kuma, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ƙasa ta nesanta kanta da jita-jitar haɗa maja da wasu jam'iyyun adawa.

sakataren watsa labaran PDP, Debo Ologunagba, ya musanta shiga tattaunawar yin maja da jam'iyyun adawan guda shida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng