A Tuna da Matattu: Sanata a Kano Ya Rabawa 'Yan Mazabarsa Likkafani da Tukwanen Kasa

A Tuna da Matattu: Sanata a Kano Ya Rabawa 'Yan Mazabarsa Likkafani da Tukwanen Kasa

  • Wani sanata a jihar Kano ya gwangwaje 'yan mazabarsa da kayayyakin yiwa mamata sutura bayan mutuwa
  • Mun samu labarin yadda aka raba tukwanen kasa 500,000 da yadin likkafani 500,000 don saukakawa dan mamata
  • Sanatan ya kuma tallafawa 'yan mazabarsa da kudaden rajistar shiga makaranta da ma jarrabawar JAMB

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Kano - Sanata daga jihar Kano, Rufaui Hango ya ba da tallafin tukwane 500,000 da yadi 500,000 na likkafani ga 'yan mazabarsa domin su samu damar binne matattunsu cikin sauki.

A cewar Hanga, ya ba da tallafin ne bayan da 'yan mazabar tasa mai dauke da kananan hukumomi 15 suka matsa lamba wajen neman taimakon kayan bison matattansu.

Kara karanta wannan

Tallafin N50,000: Gwamnati ta yi karin haske, ta fadi lokacin cigaba da biyan kudi

Dawud Auwal, wani hadimin sanatan ne ya bayyana abin da ya faru na mika tallafin ga 'yan mazabar a shafin sada zumunta na Facebook.

Sanatan Kano ya yiwa mamata hidima, ya ba da tallafin likkafani da tukwane
Yadda sanata ya tuna da matattu a mazabarsa | Hoto: Dawuud Auwal
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ake yi da irin wadannan kayayyakin?

Amfani da tukwanen kasa da likkafani ba sabon abu bane ga 'yan Arewacin Najeriya da ma wasu sassa na duniya.

Ana amfani da su ne wajen binne mamata kamar yadda addinin Islama ya koyar da kuma mutunta wadanda suka samu cikawa.

Gawar namiji Musulmi, ana mata likkafani da tufafi uku, yayin da mace ake mata tufafi biyar don rufe jiki ruf.

Wannan ne kadai aikin alherin da sanatan ya yi?

Yayin da wasu masu sharhi a kafar Facebook suka taso sanatan a gaba kan wannan aikin da suka kira abin da ba a bukata a yanzu, ya mayar da martani da karin ayyukan da sanatan ya yi.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya fayyace abin da ya tilastawa Tinubu cire tallafin man fetur

A cewarsa, sanatan ya kuma ba da tallafi a fannin ilimi ga 'yan mazabar tasa, inda ya buga misali da cewa:

"Sanatan ya kuma biyawa dalibai 200 kudin rajistar shiga jami'ar Bayero da ke Kano kana ya yiwa dalibai sama da 1000 rajistar jarrabawar JAMB. Haka nan ya tallafawa sama da 200 sun samu shiga makarantar fasaha ta Kano."

Yadda matsafa ke kutse a makabartun Kano

A wani labarin, kun ji yadda aka gano wasu matsafa na yawan shiga makabartu domin tone kaburbura a jihar Kano.

Wannan lamari dai an ruwaito cewa, ya auku ne a wani lokaci baya a wani yankin Rimin Kebe da ke jihar.

Jihohin Arewacin Najeriya na daga inda ake da saukin samun ayyukan barnar tone kaburbura a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel