Siyasar Najeriya
Wata kungiya mai rajin kawo cigaba da wayar da kan al'umma a Arewa (NAN) ta fadi yadda ake shirin wargaza APC a Zamfara saboda kin jinin Bola Tinubu.
Kotun daukaka kara ta yanke hukunci a shari'ar zaben gwamnan jihar Kogi. Kotun ta tabbatar da Usman Ododo na jam'iyyar APC a matsayin zababben gwamnan jihar.
Shugaban karamar hukumar Obio-Akpor a jihar Rivers, Chijioke Ihunwo ya yi abin a yaba kan nadin mukamai har guda 100 da ya yi kwanaki kadan bayan hawa mulki.
Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya yi martani kan wa'adin kwanaki bakwai da 'yan majalisar dokokin jihar suka ba shi. Gwamnan ya ce su ba 'yan majalisa ba ne.
Cikin masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PDP, Dakta Tom Fredfish ya bukaci manyan jam'iyyar irinsu Atiku Abubakar su saka baki wajen sasanta Fubara da Wike.
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta garzaya kotun daukaka kara kan hukuncin babbar kotun tarayya na soke zaben fidda gwaninta na gwamnan jihar Edo.
'Yan majalisar wakilai da dattawan Najeriya daga kudancin Najeriya sun mika bukatun kafa sabbin jihohi a yankunansu. Hakan zai sa a yi wa tsarin mulki kwaskwarima.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya dakatar da shugaban karamar hukumar Machina a jihar. Gwamnan ya yanke hukuncin ne bisa wasu zarge-zarge da ake yi masa.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa tsarin ilimin Najeriya ya bada gudumawar rashin aikin yi ga matasa. Dole ne a koyi sana'o'i.
Siyasar Najeriya
Samu kari