Siyasar Najeriya
Tsohon hadimin shugaban kasa, Doyin Okupe ya ce Shugaba Bola Tinubu na yin abin da ya dace kuma ƴan Najeriya za su kara ba shi dama a babban zaben 2027.
APC ta ce ba ta jefa PDP cikin rikicin cikin gida ba a Najeriya. APC ta ce gwamnan PDP ya mayar da hankali wajen kawo cigaba maimakon zargin APC.
Yayin da ya rage ƴan kwanaki a fita zaɓen gwamna a jihar Ondo, tsohon ɗan majalisar tarayya da wasu manyan ƙusoshin PDP sun haɗe da Gwamna Aiyedatiwa a APC.
Jam'iyyar APC mai mulki ta mayar da martani da Gwamna Seyi Maminde na jihar Oyo wanda bisa dukkanin alamu ya fara shirin neman karawa da Tinubu a 2027
Za a ga jerin APC da aka ji sun soki gwamnatin Bola Tinubu a Najeriya. Alal misali, sukar gwamnatin Bola Tinubu ne ya jawo Muhammad Ali Ndume ya rasa matsayinsa.
Kanin tsohon gwamnan Ekiti, Isaac Fayose ya musanta zargin da ake yaɗawa cewa ya yi kudi ne lokacin da Ayodele Fayose ke mukin jihar inda ya ce shi ɗan kasuwa ne.
Aliyu Usman Tilde ya kare ministan harkokin ilmi da aka yi waje daga majalisar FEC a watan Oktoba. Idan aka bi ta shi, Farfesa na cikin wadanda suka fi kowa kokari
Hukumar zaɓe ta kasa mai zaman kanta watau INEC ta bayyana cewa har yanzu ba ta san tsagin da yake da gaskiya ba a rikicin majalisar dokokin jihar Rivers.
Majalisar dokoki a jihar Oyo ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Oyo ta Gabas kan wani bidiyo da ke yawo wanda aka ganshi yana abubuwan da ba su dace ba.
Siyasar Najeriya
Samu kari