PDP Ta Dauki Mataki Bayan Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwaninta na Gwamna

PDP Ta Dauki Mataki Bayan Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwaninta na Gwamna

  • Jam'iyyar PDP ba ta gamsu da hukuncin babbar kotun tarayya ba na soke zaɓenn fidda gwaninta na gwamnan jihar Edo
  • PDP ta ɗaukaka ƙara a gaban kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja domin nuna adawa da hukuncin na soke takarar Asue Ighodalo
  • Babbar kotun tarayya dai da ke zamanta a jihar Edo ta soke zaɓen fidda gwanin wanda ta bayyana a matsayin mara inganci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin babbar kotun tarayya na soke zaɓen fidda gwanin gwamnan jihar Edo, wanda Asue Ighodalo, ya lashe.

Jam'iyyar PDP ta ɗaukaka ƙarar ne a gaban kotun ɗaukaka ƙara da ke birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dauki matakin magance yunwar da ake yi a kasa

Jam'iyyar PDP ta daukaka kara kan hukuncin kotu
PDP ta daukaka kara kan soke zaben fidda gwanin gwamnan jihar Edo Hoto: Asue Ighodalo
Asali: Facebook

PDP a ƙarar da ta shigar kan dalilai 25, ta buƙaci kotun ɗaukaka ƙara da ta yi watsi da hukuncin da karamar kotun ta yanke a ranar 4 ga watan Yuli, 2024, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ku tuna cewa mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya bayyana zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP da aka gudanar a ranar 22 ga watan Fabrairu a jihar Edo a matsayin mara inganci.

Zaɓen Edo: PDP ta ɗaukaka ƙara

PDP, a ƙarar da ta shigar a ranar 9 ga watan Yuli mai lamba CA/ABJ/CV/2024 ta hannun lauyanta Adeyemi Ajibade (SAN), ta ce hukuncin da kotun ta yanke ya ci karo da shaidun da aka gabatar, rahoton Osundefender ya tabbatar.

Waɗanda ake kara a ƙarar sun haɗa da Kelvin Mohammed, Gabriel Okoduwa, Ederaho Osagie, hukumar INEC, sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa, da mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa yankin Kudu-maso-Kudu.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan tsige 'yan majalisa 25 da suka sauya bar PDP zuwa APC

PDP ta ce a ranar 4 ga watan Fabarairu ta gudanar da zaɓen deliget a ƙananan hukumomi 18 na jihar, kuma waɗanda ake ƙara na ɗaya zuwa na uku ba su shiga zaɓen ba kuma ba su daga cikin waɗanda suka zama deliget.

Jam'iyyar ta bayyana deliget ɗin ta da suka gudanar da zaɓen fidda gwani ne suka zaɓi Asue Ighodalo a matsayin ɗan takararta na gwamna.

APC ta shirya murƙushe PDP a Edo

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Adams Oshiomole ya sha alwashin lashe zaɓen gwamnan jihar Edo.

Adams Oshiomole ya ce duk da rusa zaben fidda gwanin jami'yyar PDP da kotu ta yi a jihar, ba za su yi wasa da damar kawo ƙarshen mulkin PDP a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng