"Kun Rasa Kujerunku": Gwamnan PDP Ya Yi Martani Bayan 'Yan Majalisa Sun Ba Shi Wa'adin Kwana 7

"Kun Rasa Kujerunku": Gwamnan PDP Ya Yi Martani Bayan 'Yan Majalisa Sun Ba Shi Wa'adin Kwana 7

  • Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya ɗauki ɗamarar yaƙi da ƴan majalisar da suka sauya sheƙa ƙarƙashin jagorancin Martins Amaewhule
  • Gwamna Siminalayi Fubara ya bayyana cewa kwanan nan gwamnatinsa za ta fara shirin haɗa kasafin kuɗin shekarar 2025
  • Hakan na zuwa ne bayan ƴan majalisar ƙarƙashin jagorancin Martins Amaewhule sun ba shi wa'adin kwanaki bakwai da ya sake gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2024 a gabansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya ce zai gabatar da ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2025 ga majalisar dokokin jihar nan ba da jimawa ba.

Gwamna Fubara ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan wa’adin kwanaki bakwai da ƴan majalisar dokokin jihar masu biyayya ga Nyesom Wike, suka ba shi.

Kara karanta wannan

Ba a gama da Betta Edu ba, majalisa ta titsiye ministar Tinubu kan badakalar N1.5bn

Fubara ya caccaki 'yan majalisa masu goyon bayan Wike
Gwamna Fubara ya ce Martins Amaewhule da sauran 'yan majalisa masu biyayya ga Wike sun rasa kujerunsu Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Martins Amaewhule
Asali: Facebook

Yayin zaman majalisar a ranar Litinin, ƴan majalisar sun buƙaci Gwamna Fubara da ya sake gabatar da kasafin kuɗin jihar na 2024 cikin kwanaki bakwai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Fubara ya ce kan kasafin kuɗi?

Sai dai, a ranar Laraba, Gwamna Fubara ya ce ya gama da batun kasafin kuɗin 2024 kuma ƴan majalisar masu biyayya ga Wike da suka koma APC sun rasa kujerunsu, cewar rahoton jaridar The Cable.

Gwamna Fubara ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga wata tawaga daga ƙananan hukumomin Etche da Omuma waɗanda suka kai masa ziyara a gidan gwamnati da ke Port Harcourt a ranar Laraba.

Fubara ya yi watsi da masu biyayya ga Wike

Ya buƙaci mutane da su yi watsi da abin da ƴan majalisar suke cewa, inda ya ce su ɗin ba halastattu ba ne, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya ba tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega sabon mukami

"Dukkaninmu mun san yadda suka tsallaka zuwa APC. Ta yaya suka sauya sheƙa? Saboda ubangiji ne. Domin yin wannan kuskuren da suka yi, sun tafi an wuce da batunsu."
"Lokacin da na ke son na taimake su, na amince na taimake su saboda mu duka ƴan uwa ne. Za mu iya saɓawa. Amma sun ɗauka ce su masu wayau ne."
"Abin da kawai yake riƙe da su shi ne ayyana kujerunsu a matsayin waɗanda babu kowa a kai, wanda aka yi a watan Disamban 2023."
"Ni a wajena na fara shirya kasafin kuɗin shekarar 2025, wanda zan gabatar nan ba da jimawa ba."
"Kada ku bari wani ya yaudare ku. Za su iya zuwa gaban ƴan jarida su yi ta surutu. Amma da sun bar wajen kuka suke yi. Wannan shi ne gaskiya."

- Siminalayi Fubara

Shehu Sani ya magantu kan rikicin Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya yi magana kan rikicin siyasar da ke tsakanin gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da magabacinsa, Nyesom Wike.

Shehu Sani ya bayyana cewa Allah ne kaɗai zai iya magance rikicin siyasar da ke tsakanin mutanen biyu waɗanda ba sa ga maciji da juna a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng