Shugaban Sojojin Najeriya
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya jinjinawa shugaba Bola Tinubu kan nadin sabbin shugabannnin tsaro da Nuhu Ribasu a matsayin mai ba kasa shawara kan tsaro.
Kotun daukaka kara ta ce an sauke shugaban hukumar ta NIA ne ba tare da bin doka ba. Bayan shekaru 5, Alkali ya dawo da tsohon Shugaban NIA a kan kujerarsa.
DSS ta ankarar da al’umma cewa akwai shirye-shirye aukawa wuraren bauta da filayen wasanni. Dr. Peter Afunanya ya ce DSS da Sojoji da ‘Yan Sanda sun gano hakan.
Hedkwatar rundunar sojin ruwa ta karyata zargin da ake yi cewa shugaban rundunar mai barin gado, Awwal Gambo, ya ki mika mulki ga magajinsa, Emmanuel Ogalla.
An ji labari cewa nadin Manjo Janar Christopher Musa da su Taoreed Lagbaja zai canza shugabancin sojojin Najeriya. Sojoji da-dama za su sake ajiye khakinsu.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya tsige dukkanin shugabannin rundunar sojoji sannan ya nada Janar Taoreed Abiodun Lagbaja a matsayin sabon babban hafsan sojoji.
Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin sabbin hafsoshin soji, sufeto janar na yan sanda da kwanturola Janar na Kwastam a ranar Litinin.
An samu hafsoshin sojoji da sauran manyan jami’an tsaro. Za a ji Bola Tinubu ya kafa tarihi wajen nada guraye da wanda ya kwato $8m a matsayin Hafsoshin Tsaro
Akalla mutane goma sha biyar ne rahotanni suka kawo cewa an yi wa yankan rago a wani hari da wasu da ake kyautata zaton yan Boko Haram ne suka kai jihar Borno.
Shugaban Sojojin Najeriya
Samu kari