Haduran mota a Najeriya
Wani mummunan hatsarin tsautsayi ya yi ajalin mata biyar yayin da kwantenar da babbar motar dakon kaya ta ɗauƙo ta faɗa wa Motar bas a babban titin Anambra.
Wani jami'in Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa, FRSC ya rasa ransa bayan direban babbar mota ya tunkudo shi kasa tare da murkushe shi har lahira a hanyar Abuja.
A dalilin tashin da litar man fetur ta yi, Gwamnatin jihar Edo ta samar da motoci domin hawa kyauta. Za a shafe tsawon makonni ana cin moriyar tsarin.
Wata babbar mota ta murkushe wata mata mai ciki da raunata danta mai shekaru biyu a cikin kasuwa da ke jihar Ogun, motar ta kutsa cikin kasuwa bayan birki ya balle.
Wani hatsarin mota ya ritsa da wani ɗan Achaɓa ɗauke da fasinjoji a jihar Kwara. Dan Achaban ya rasu ne bayan motar tirelar ta murƙushe shi a hatsarin.
Jimami yayin da hatsarin mota ya yi ajalin wasu mutane shida a kan hanyar Akure zuwa Owo da ke jihar Ondo, hukumar FRSC ta kwashi gawarwakin zuwa asibitin jihar
Wasu munanan haɗuran mota da suka auku sun salwantar da rayukan mutum takwas a jihohin Ogun da Ondo. Haɗuran sun auku ne a dalilin gudu wanda ya wuce ƙa'ida.
Wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da wasu bayin Allah a jihar Osun. An salwantar da rayukan mutane masu yawa a dalilin hatsarin motar da ya auku cikin dare.
Wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Ondo, ya salwantar da rayukan mutum. Wasu mutum biyar kuma sum samu munanan raunika a dalilin hatsarin motar.
Haduran mota a Najeriya
Samu kari