Ana Zargin Yana Tare da APC, Kwankwaso Ya bada Shawara kan Sake Zaben Tinubu a 2027

Ana Zargin Yana Tare da APC, Kwankwaso Ya bada Shawara kan Sake Zaben Tinubu a 2027

  • Rabiu Kwankwaso ya ce gwamnatin Tinubu da ta gaza kare rayuka da dukiyoyin jama’a ba ta cancanci a sake ba ta wa’adin mulki na biyu ba
  • Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC ya ce tikitinsu da Peter Obi na da manufar haɗa kan ’yan Najeriya
  • Ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsu za ta mayar da hankali kan yaƙi da rashin tsaro, talauci da jahilci, tare da zuba jari a noma da ilimi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Sanata Rabiu Kwankwaso, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Kwankwaso ya nuna damuwa kan yadda gwamnati mai ci take tafiyar da matsalar rashin tsaro da talauci.

Kwankwaso.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Source: Facebook

A rahoton Leadership, Kwankwaso ya ce ya ce duk gwamnatin da ta gaza kare rayuka da dukiyoyin jama’a ba ta cancanci a sake ba ta wa’adin mulki na biyu ba.

Kara karanta wannan

Makinde ya faɗi dalilin ƙalubakantar Tinubu duk da sun fito daga yanki ɗaya

Kwankwaso ya wakilci Peter Obi

Kwankwaso, tsohon gwamnan Jihar Kano kuma tsohon ministan tsaro, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Jos, babban birnin Jihar Filato, a wani babban taron tattaunawa da jama’a.

Taron, wanda Big Tent, Obidient Movement, Kwankwasiyya Movement da shugabannin NDC suka mara wa baya, an shirya cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi, ne zai jagoranta, amma bai samu halarta ba, inda Kwankwaso ya wakilce shi.

Da yake jawabi ga magoya baya, Kwankwaso ya ce gwamnati Tinubu ta gaza magance ƙalubalen tsaro da matsin tattalin arziƙin da ƙasar ke fuskanta.

Shawarar Kwankwaso ga yan Najeriya

Ya jaddada cewa ’yan Najeriya na buƙatar shugabannin da suka himmatu wajen kare rayukansu da inganta walwalarsu.

“Duk gwamnatin da ba za ta iya yin hakan ba, ba za mu kira ta gwamnati mai sauke nauyinta ba kuma irin wannan gwamnati ba ta cancanci a sake zabenta a wa’adin mulki na biyu ba,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya jingine bambancin siyasa, ya aika da muhimmin sako ga Kwankwaso

Dalilin rashin halartar Obi

Da yake bayyana dalilin da ya sa Obi bai halarci taron ba, Kwankwaso ya ce an samu tsaiko ne ga tsohon gwamnan Jihar Anambra a Enugu saboda wasu yanayi da ba ya da iko a kansu.

Ya ce:

“An shirya cewa mai girma Peter Obi, wanda shi ne ɗan takararmu na shugaban ƙasa, zai jagoranci wannan taro. Amma da sassafe, ya kira ni ya aiko da saƙo cewa ya makale a Enugu, kuma saboda yanayi ba zai iya zuwa Filato ba.
“Amma abu ɗaya da muka amince da shi shi ne cewa nan ba da jimawa ba za mu tsara wata rana domin mu zo tare, mu yi muku cikakken bayani a wannan zaure.”
Kwankwaso.
Tawagar Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso lokacin da suka isa jihar Sakkwato Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Kwankwaso ya bayyana tikitin Obi da shi a matsayin tikitin haɗin kai da daidaito, yana mai cewa zai haɗa ’yan Najeriya daga yankuna, addinai da ƙabilu daban-daban.

Tinubu ya taya Kwankwaso murna

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya taya dan takarar mataimakin shugaban kasar na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso murnar cika shekara 70 da haihuwa a duniya.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa ya nemi aron Aso Rock domin kaddamar da kamfen

A cikin sakon, Tinubu ya bayyana Kwankwaso a matsayin abokinsa, ɗan siyasa mai tasiri kuma mai ra’ayin kawo ci gaba.

Tinubu ya ce alaƙarsa da Kwankwaso ta samo asali ne tun shekarar 1992, lokacin da suke Majalisar Dokoki ta Ƙasa, inda Kwankwaso yake a Majalisar Wakilai, shi kuma Tinubu yake a Majalisar Dattawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262