Matsala Sabuwa Ta Tunkaro Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
- SERAP ta shigar da ƙara kan gwamnatin tarayya bisa zargin rashin bin ƙa’ida wajen rabon kudaden tallafi
- Rahoton babban mai binciken kuɗi na tarayya ya nuna akwai kuɗaɗen da ba a samu isassun takardun tabbatar da biyan su ba
- Ƙungiyar ta nemi kotun ta umarci gwamnati ta bayyana yadda aka kashe kuɗin, ta gudanar da bincike tare da dawo da duk kuɗin da aka karkatar ba bisa ƙa’ida ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ƙungiyar kare haƙƙin tattalin arziki da zamantakewa da tabbatar da riƙon amana, SERAP, ta shigar da ƙara kan gwamnatin tarayya a Kotun ECOWAS.
SERAP ta shigar da karar ne kan zargin rashin bin ƙa’ida wajen sarrafa sama da Naira biliyan 78.8 da aka ware wa shirye-shiryen tallafin kuɗi da kare masu karamin karfi.

Kara karanta wannan
Da gaske an fitar da Naira tiriliyan 2.3 don ƙaddamar da kamfen APC a Kaduna? Gaskiya ta fito

Source: Facebook
Ƙarar, mai lamba ECW/CCJ/APP/42/26, an shigar da ita ne a makon da ya gabata, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Ƙungiyar ta ce zarge-zargen sun shafi Ma’aikatar Jin Kai da Rage Talauci, Ofishin Kula da Tallafin Kuɗi na Ƙasa (NCTO) da kuma Ofishin Haɗa Ayyukan Tsaron Zamantakewa na Ƙasa (NASSCO).
A cewar SERAP, an rubuta matsalolin a cikin rahoton shekara na 2024 na babban mai binciken kuɗi na tarayya, wanda aka wallafa a ranar 7 ga Agusta, 2026. Rahoton ya ƙunshi bayanan lokuta daban-daban tsakanin Janairu 2023 zuwa 31 ga Disamba, 2024.
Abin da SERAP ke nema a kotu
SERAP na neman kotun ta bayyana cewa rashin bayar da cikakken bayani kan kuɗaɗen da aka ware wa shirye-shiryen tallafin kuɗi da kare masu rauni ya saɓa wa wajibcin Najeriya na kare haƙƙin ɗan Adam a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa.
Ƙungiyar ta kuma nemi kotun ta umarci gwamnati ta gabatar da cikakken bayani mai inganci kuma wanda za a iya tantancewa kan kuɗaɗen da ake tambaya, The Punch ta kawo labarin.
Bayanan da take son a bayyana sun haɗa da takardun biyan kuɗi, sunayen waɗanda suka amfana, takardun tantance masu karɓar tallafi da kuma bayanan da ke nuna yadda aka daidaita asusun kuɗaɗen.
Haka kuma, SERAP na neman a gudanar da bincike mai zaman kansa kan zarge-zargen, a dawo da duk kuɗin gwamnati da aka tabbatar an kashe ko karkatar da su ba bisa ƙa’ida ba, sannan a ɗauki matakan shari’a ko na gudanarwa kan waɗanda aka samu da laifi bisa ƙa’ida.
Rahoton ya nuna matsaloli a biyan biliyoyin Naira
A cewar SERAP, rahoton babban mai binciken kuɗi ya yi tambaya kan kusan Naira biliyan 33.751 da aka ce an tura wa gidaje sama da miliyan 3.2 a jihohi 35 a shekarar 2023.
Rahoton ya nuna cewa babu isassun takardu da za su tabbatar da biyan kuɗaɗen tare da daidaita bayanan waɗanda aka ce sun amfana.
Haka kuma, rahoton ya nuna akwai kuɗaɗen da ake zargin an biya ba tare da tantance su kafin biyan kuɗi ba, waɗanda suka kai Naira biliyan 36.744, da kuma kashe kuɗi na Naira biliyan 4.616 da ba a samu takardun da suka tabbatar da ingancinsu ba.
Sauran kuɗaɗen da aka yi tambaya a kansu sun haɗa da: Naira miliyan 350.182 da aka ware wa rajistar masu cin gajiyar shirin. Naira miliyan 89.511 da aka kashe wajen sayen kayayyakin ajiya. Naira miliyan 17.422 da aka bayar a matsayin kuɗin sayen man dizal.
SERAP ta ce waɗannan bayanai sun haifar da tambayoyi kan yadda aka sarrafa kuɗaɗen da kuma ko tallafin ya isa ga mutanen da aka tsara domin su amfana.

Source: Facebook
SERAP ta maka Tinubu a kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar kare hakkokin tattalin arziki da tattalin arziki (SERAP) ta maka Shugaba Bola Tinubu a gaban kotu.
An ce SERAP ta yi karar Tinubu ne bayan da ya gaza janye karin kudin man fetur da NNPCL ya yi da kuma gaza bincikar kamfanin man.
Asali: Legit.ng

