Jam'iyyar PDP
Mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Umar Iliya Damagum ya aika da sakon gargadi ga masu yi wa PDP zagon kasa. Ya ce za su dauki matakin ladabtarwa.
A labarin nan, za a ji cewa wasu daga cikin manyan yan siyasa a jam'iyya mai mulki ta APC da ta adawa, PDP na sauya sheka zuwa sabuwar jam'iyyar hadaka, ADC.
Fadar shugaban kasa ta ce nan da wata 6 masu hadaka a jam'iyyar ADC za su tarwatse a fadin Najeriya. Daniel Bwala ya ce zaben 2027 ne mafi sauki ga Tinubu.
Tsohon shugaban PDP na jihar Katsina, Hon. Salisu Lawal Uli, ya ce ya gaji da zama a jam'iyyar da shugabancinta ke tangal tangal, ya sanar da komawa haɗakar ADC.
Adamu Waziri, tsohon ministan Najeriya, ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa ADC don neman shugabanci na nagar saboda damuwar rashin tsaro da halin tattalin arziki.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana yiwuwar sake tsayawa takarar shugabancin Najeriya a 2027 yayin da ya karɓi wata tawaga a Abuja.
Tsohon ɗan takarar gwamnan Kaduna a inuwar PDP, Hon. Isah Ashiru Kudan ya ce a shirye yake ya shiga kowace irin haɗaka don kawo karshen mulkin APC a 2027.
Kowane ɗan Najeriya yana da damar yin rijista da duk jam'iyyar siyasar da ta kwanta masa a rai, ta yi daidai da manufofinsa, misali kamar APC, PDP ko ADC.
Yayin da yan siyasa da dama suka sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC a Zamfara, shugabanta a jihar, Kabiru Garba, ya gayyaci Gwamna Dauda Lawal da ya sauya sheka.
Jam'iyyar PDP
Samu kari