Jam'iyyar PDP
Jam’iyyar APC reshen jihar Ribas ta bayyana a ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba, cewa duk kokarin sulhunta Fubara da Wike da Tinubu ya yi bai cimma nasara ba.
Tony Adoki daya daga cikin yan majalisar dokokin jihar Rivers ya yi magana kan sake komawa PDP, yan kwanaki kadan bayan ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Mai shari’a Abdulaziz Waziri na kotun daukaka kara ya bayyana ainahin dalilin da yasa aka tsige yan majalisar jihar Filato 16, yana mai karin haske kan hukuncin.
Jam’iyyar PDP a jihar Oyo tana shirin kara samun gagarumin karfi yayin da Shina Peller, tsohon dan majalisar wakilai kuma tsohon jigon APC ke shirin komawa cikinta.
Dan takarar Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Usman Ibrahim ya yi fatali da jami'yyar PDP inda ya koma jam'iyya mai mulki ta APC a jihar, ya yabawa salon mulkin Uba Sani.
Babban lauya Femi Falana (SAN) ya yi magana kan rikicin da ya dabaibaye majalisar dokokin jihar Rivers. Falana ya fadi makomar yan majalisar da suka koma APC.
Tsohon mataimakin kakakin Majalisar Ebonyi, Odefa Obasi Odefa ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC da wasu magoya bayansa 500 a mazabar Onicha ta Gabas.
Gwamna Siminalayi Fubara ya taya murna ga Ministan Abuja, Nyesom Wike a ranar bikin zagayowar haihuwarsa duk da irin alaka mai tsami da ke tsakaninsu.
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 a gaban mambobin Majalisar jihar guda biyar kacal bayan sauran sun sauya sheka.
Jam'iyyar PDP
Samu kari