Karin Bayani: Kwamishinoni Huɗu Sun Yi Murabus Daga Muƙamansu a Jihar PDP, Sun Faɗi Dalili

Karin Bayani: Kwamishinoni Huɗu Sun Yi Murabus Daga Muƙamansu a Jihar PDP, Sun Faɗi Dalili

  • Karin kwamishinoni huɗu sun yi murabus daga kan muƙamansu awanni bayan Antoni Janar ya yi murabus a jihar Ribas
  • Wannan na zuwa ne yayin da rigima ke ƙara tsanani tsakanin gwamna mai ci, Siminalayi Fubara, da ministan Abuja, Nyesom Wike
  • A cewar kwamishinonin sun yi murabus ne bisa dalilin kai da kai kuma sun gode wa Gwamna Fubara tare da fatan alheri

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Yayin da alamu ke nuna rikicin siyasar jihar Ribas ya ƙara tsananta, ƙarin kwamishinoni hudu sun yi murabus daga kan muƙamansu.

Rahoton Daily Trust ya tattaro cewa waɗanda suka yi murabus ɗin sun haɗa da kwamishinan ayyuka kuma ɗan amutun tsohon gwamna, Nyesom Wike, Dakta George-Kelly Alabo.

Kara karanta wannan

Babbar matsala ga gwamna yayin da ƴan majalisa 26 suka yi zama na musamman, bayanai sun fito

Karin kwamishinoni sun aje aiki a Ribas.
Rivers: Kwamishinoni Biyu Sun Yi Murabus Yayin da Rikicin Wike da Fubara Ya Kara Tsanani Hoto: Fubara, Nyesom Wike
Asali: Facebook

Sauran sune, kwamishinar ma'aikatar walwala da jin daɗi, Misis Inime Chinwenwo-Aguma, kwamishinan kuɗi, Isaac Kamalu da kwamishinan ayyuka na musamman, Emeka Woke.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alabo ya tabbatar da matakin yin murabus daga matsayin kwamishinan ayyuka na Ribas a wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 14 ga watan Disamba, 2023.

Ya kuma aika wasiƙar murabus ɗin ga Gwamna Siminalayi Fubara ta hannun sakataren gwamnatin jihar.

A wasiƙar, Mista Alabi, wanda ya yi aiki a matsayin Kwamishinan Ayyuka a gwamnatin Wike, ya ce ya yi murabus ne bisa ra'ayin kansa.

Meyasa kwamishinonin suka yi murabus?

Dakta Alabo, a wasiƙar mai taken, "Murabus daga matsayin kwamishinan ayyuka na jihar Ribas," ya ce:

"Matakin da na ɗauka na yin murabus ya dogara ne a kan lamirina, ra'ayi da falsafar kaina, da kuma ɗabi'ar ƙwararru. Na dauki wannan matakin ne bayan zurfafa tunani."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya bada mamaki kwana daya bayan miƙa kasafin kuɗin 2024 ga majalisa

Haka nan kuma ya gode wa Gwamna Fubara bisa damar da ya ba shi ta yin aiki a ƙarƙashin gwamnatinsa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A nata bangaren, Kwamishinar walwala da jin daɗi ta ce ta yi murabus ne bisa wasu dalilai na ƙashin kanta kana ta yi wa gwamnati mai ci fatan alkairi.

Alabo da Chinwenwo-Aguma sun yi murabus ne sa’o’i kaɗan bayan kwamishinan shari’a kuma Antoni Janar na jihar, Farfesa Zacchaeus Adangor ya yi murabus daga mukaminsa.

Gwamna Obaseki ya faɗi ɗan taƙararsa a zaben Edo

A wani rahoton kuma Gwamna Godwin Obaseki ya bayyana ɗan takarar da zai marawa baya a zaben gwamnan jihar mai zuwa a shekarar 2024.

Obaseki ya ayyana cewa babu wata matsala tsakaninsa da mataimakinsa, Philip Shuaibu, wanda ke neman gaje shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel