Rikicin PDP
Kwamitin mutum bakwai da babban alkalin jihar Edo ya kafa ya fara zaman domin bincike kan zargin da majalisar dokoki ke wa mataimakin gwamna, Shaibu.
Gwamna Sir Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya yi ikirarin cewa babu abin da zai dakatar da gwamnatinsa daga kammala wa'adinta na shekaru 4 a jihar.
Mambobi 6 na majalisar dokokin jihar Enugu sun sauya sheka daga Labour Party da aka zaɓe su karkashinta, sun koma jam'iyyar PDP mai mulkin jihar kan wani daili.
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sha alwashin hukunta 'ya'yanta da suka ci dunduniyarta a lokacin babban zaben da aka gudanar a shekarar 2023.
Babban alkalin jihar Edo, mai shari'a D. I. Okungbowa, ya kafa kwamitin mutane 7 da zasu gudanar da bincike kan zargin da majalisar take wa mataimakin gwamna.
Kwamared Philip Shaibu ya yi rashin nasara a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja a kokarin dakatar da majalisar dokoki daga yunkurin tsige shi a jihar Edo.
Majalisar dokokin jihar Edo ta umurci alkalin alkalan jihar samar da kwamitin mutanen da za su duba zarge-zargen da ake yi wa mataimakin gwamnan jihar don tsige shi.
Stanley Ekezie, wani jigo a jam'iyyar PDP a jihar Imo, ya ce masu zaɓe ne suka jefa Najeriya a mawuyacin halin da take ciki ta hanyar zaben gurbatattun 'yan siyasa.
Tsohon mai magana da yawun rusasshen kwamitin kamfen Atiku/Okowa na PDP, Daniel Bwala ya ce saida Najeriya sannan ƴan siyasa za su sanu fagen fafatawa.
Rikicin PDP
Samu kari