Sabon Rikici Ya Barke a Jam’iyyar PDP, Atiku Da Wasu Gwamnoni Sun Fara Takun Saka Mai Zafi

Sabon Rikici Ya Barke a Jam’iyyar PDP, Atiku Da Wasu Gwamnoni Sun Fara Takun Saka Mai Zafi

  • Da alama rikicin cikin gida na jam'iyyar PDP ba mai karewa ba ne don yanzu, rikicin shugabanci ya sake ballewa a jam'iyyar
  • Ana zargin cewa jiga-jigan jam'iyyar da suka hada da Atiku Abubakar na kokarin kwace ragamar shugabancin jam'iyyar
  • Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya fara tsanani tun bayan shan kauye a Kotun Koli kan zaben shugaban kasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sake fadawa cikin wani sabon rikici, wanda ya tilasta tsayawar duk wasu ayyukan gudanar da jam'iyyar.

A cewar wani rahoto na The Sun, jiga-jigan jam'iyyar na fada ne kan shugabanci, tun bayan kammala zaben 2023 da suka sha kaye hannun APC.

Kara karanta wannan

Ganduje ya sake yi wa jam'iyyar PDP lahani a arewa yayin da ake jiran hukuncin Kotun Koli

Atiku da wasu gwamnonin PDP
Sabon rikici ya balle a PDP, Atiku da wasu gwamnoni na son kwace jam'iyyar Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Yadda rikici ya mamaye jam'iyyar PDP

Korar karar da PDP ta shigar a Kotun Koli kan zaben shugaban kasa, da ma sauran kararrakin zaben da ta rasa, ya fara haddasa rikicin cikin gida a jam'iyyar, rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da sun rasa shugabanci a 2023, sai jiga-jigan suka fara tunanin yadda za su tunkari zaben 2027, wanda kowa ke kokarin rike ikon gudanarwar jam'iyyar.

Yadda Wike da Makinde suka shiga rikicin

An ruwaito cewa akwai baraka a kungiyar G5 karkashin jagorancin ministan Abuja, Nyesom Wike, inda aka yi kokarin tsige Samuel Anyanwu, sakataren PDP na kasa, kotu ta dakatar.

Yayin da Anyanwu ke goyon bayan Wike, shi kuma Odefa (mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa) yana goyon bayan Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo.

Wani tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, Cosmas Ndukwe, ya ce abin takaici ne yadda shugabannin jam'iyyar ke rikici kan wanda zai zama shugaba da sakataren jam'iyyar na kasa.

Kara karanta wannan

"Abin da zai faru a zaben 2027 idan jam'iyyun adawa ba su hada kai ba", jigon PDP ya yi hasashe

An dakatar da shugaban PDP a Imo saboda zagon kasa

A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa jam'iyyar PDP ta dakatar da shugaban ta na jihar Imo, Engr. Charles Ugwu.

Masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a jihar ne suka yi zama, inda suka kada kuri'ar rashin cancanta kan iya rikon shugabancin jam'iyyar.

Akalla shugabannin kananan hukumomi 18 da mambobin kwamitin zartaswar jam'iyyar ne suka saka hannu kan takardar tsige Agwu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel