Sarkin Kano
A cewar wata sanarwa, Gwamna Abba Yusuf ya ce mayar da Muhammadu Sanusi II gidan sarautar Kano na daga cikin alkawurran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe.
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya umarci korarrun sarakuna guda biyar da suka rasa kujerunsu da su fice daga fada cikin sa'o'i 48 masu zuwa.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya yi shaguɓe ga Sarki Muhammadu Sanusi II a wani tsohon faifan bidiyo bayan tube shi a sarautar jihar.
Majalisar dokokin jihar Kano ta sanar da rusa dokar masarautu da Ganduje ya kirkiro tare da dawo da Muhammadu Sanusi II. Abubuwa uku sun ja hankalin al'umma.
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya sanya hannu a dokar da ta rusa masarautun jihar guda biyar da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro a shekarar 2019.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya shiga ganawar sirri da 'yan majalisar dokokin jihar da masu zaben Sarki a fadar gwamnatin jihar da ke birnin Kano.
Mai martaba Sarkin Kano na 14, Malam Muhammadu Sunusi II ya gaggauta barin wani taro da ya halarta a jihar Rivers a yau bayan labarin mayar da shi karagarsa.
Awanni kadan bayan rusa masarautun jihar Kano guda biyar da Majalisar dokoki ta yi, masu nadin sarauta sun shiga gidan gwamnati domin nada sabon Sarki.
Biyo bayan rusa masarautu da majalisar dokokin jihar Kano ta yi, hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya ce lamarin ba zai kawo cigaba ba.
Sarkin Kano
Samu kari