Rudani Yayin da Tsohon Sarki Aminu Ado Bayero Ya Koma Fada a Kano, Bidiyo Ya Fito

Rudani Yayin da Tsohon Sarki Aminu Ado Bayero Ya Koma Fada a Kano, Bidiyo Ya Fito

  • Tsohon Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya isa birnin Kano kwanaki biyu bayan gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya sauke shi daga sarauta
  • Aminu Ado Bayero ya koma fadar Sarki da ke Nasarawa inda ya samu tarba daga ɗumbin magoya bayansa
  • Komawarsa fadar na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir ya ba da umarnin a cafke shi saboda zargin da ya yi masa na ƙoƙarin kawo rikici a jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Kano na 15, ya koma wata fada a cikin birnin Kano.

Tsohon Sarkin na Kano ya koma birnin ne da sanyin safiyar ranar Asabar.

Aminu Ado Bayero ya koma fada a Kano
Aminu Ado Bayero ya koma wata fada a Kano Hoto: @aaibrahim92
Asali: Twitter

Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya kori Aminu Ado Bayero tare da sauran Sarakuna huɗu da magabacinsa Abdullahi Ganduje ya naɗa, ya ba su sa’o’i 48 da su bar fadarsu.

Kara karanta wannan

Kano: Sojoji sun ja daga yayin da Abba Kabir ya umarci cafke Aminu Ado Bayero

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga nan ne ya ba da sanarwar naɗa Alhaji Muhammadu Sanusi II wanda Ganduje ya tsige shi a shekarar 2020 a matsayin sabon Sarkin Kano.

Yaushe Aminu Ado Bayero ya koma Kano?

Sai dai, da sanyin safiyar Asabar, Aminu Ado Bayero ya koma Kano inda ɗimbin magoya bayansa suka tarbe shi, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Daga baya ya koma ƙaramar fadar da ke Nasarawa, lamarin da ya haifar da ruɗani.

Sai dai, Muhammadu Sanusi II yana babbar fadar Sarkin ta Gidan Rumfa. A yanzu haka dai gidajen Sarkin biyu na ƙarƙashin tsaro sosai.

A baya dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya buƙaci jami’an tsaro da su kama Aminu Ado Bayero wanda ya zarga da haifar da rikici a jihar.

Umarnin Kama Aminu Ado Bayero

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin a kama tsohon sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ba tare da ɓata lokaci ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya ɗauki zafi, ya ba da umarnin a kama tsohon Sarkin Kano

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a Asabar, 25 ga watan Mayu.

Gwamna Abba Kabir ya zargi tsohon sarkin da aka tsige da yunƙurin ta da zaune tsaye da haifar da tashin hankali a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel