Sanusi II Ya Aika Sako Ga Ganduje Bayan Ya Dawo Kan Sarautar Kano

Sanusi II Ya Aika Sako Ga Ganduje Bayan Ya Dawo Kan Sarautar Kano

  • Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ki yin magana kan masu hannu a tuɓe shi daga kan sarautar Kano a shekarar 2020
  • Sanusi II ya bayyana cewa waɗanda suka yi masa hakan, ba su.kai darajar da zai yi magana a kansu ba
  • Sabon Sarkin na Kano ya kuma nuna godiyarsa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ƴan majalisar dokokin jihar bisa dawo da shi kan sarauta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi fatali da yin magana kan masu hannu a tuɓe masa rawani a shekarar 2020.

Sabon Sarkin na Kano ya bayyana cewa ba su kai darajar da za a yi magana a kansu ba.

Kara karanta wannan

Rudani yayin da tsohon Sarki Aminu Ado Bayero ya koma fada a Kano, bidiyo ya fito

Sanusi II ya yi magana kan tube shi a 2020
Sanusi II ya zama sabon Sarkin Kano a karo na biyu Hoto: @MSII_dynasty
Asali: Twitter

Sanusi II ya rasa sarautar Kano ne a shekarar 2020 bayan gwamnan jihar na wancan lokacin, Abdullahi Umar Ganduje ya sauke shi saboda wasu zarge-zarge.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shekara huɗu bayan hakan, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dawo da Sanusi II kan sarauta bayan soke dokar masarautu ta 2019 da kafa dokar masarautu ta 2024.

Gwamnan ya ce matakin da gwamnatinsa ta ɗauka ta yi ne domin dawo da martabar masarautar Kano bayan an tsinkata zuwa gida biyar.

Me Sanusi II ya ce kan masu tsige shi?

Jaridar Leadership ta ce jim kaɗan bayan gabatar masa da takardar naɗinsa a gidan gwamnatin jihar Kano a ranar Juma'a, Sanusi II ya bayyana cewa:

“Waɗanda suka yi hakan ba su kai darajar da zan yi magana a kan abin da suka yi ba."

Mai martaba Sarkin ya nuna godiyarsa ga Gwamna Abba da ƴan majalisar dokokin jihar bisa matakin da suka ɗauka na dawo da shi kan sarauta, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Muhammadu Sanusi II: Abubuwa 7 da suka faru a rayuwar Sarki bayan tube shi a 2020

"Gwamna da ƴan majalisarmu, ba za ku fahimci girman abin da kuka yi wa tarihin Kano da ma ƙasa baki ɗaya ba. Allah ya ƙaddara lokaci da dalili akan komai da kowa."
"Yana ba da mulki ga wanda ya so kuma a lokacin da ya so. Idan ya ba da, babu wanda ya isa ya ƙwace, sannan idan ya ƙwace babu wanda ya isa ya dawo da shi."

- Muhammadu Sanusi II

Sanusi II ya jagoranci Sallah

A wani labarin kuma, kun ji cewa sabon Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya jagoranci sallar Juma'a a masallacin dake fadar gwamnatin Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana cewa Sanusi II ne zai jagorance su sallah jim kaɗan bayan tabbatar da shi a matsayin sabon sarkin Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel