Jigon APC ya Aikawa Sanusi II Saƙo Ganin Abba Ya Dawo da shi Karagar Sarautar Kano

Jigon APC ya Aikawa Sanusi II Saƙo Ganin Abba Ya Dawo da shi Karagar Sarautar Kano

  • A ra’ayin Muazu Magaji, tun farko siyasa ta jawo aka barka masarautar Kano lokacin mulkin Abdullahi Ganduje
  • Tsohon kwamishinan ayyukan na Kano ya tura sako zuwa ga Mai martaba Muhammadu Sanusi II bayan dawowarsa
  • Dansarauniya wanda ya nemi tikitin gwamnan Kano a 2023 ya ce za suyi biyayya ga Sanusi II idan mulki zai yi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Muazu Magaji Dansarauniya bai saba ganin abubuwa ya yi tsit ba, tun da aka fara gyara dokar masarautun Kano yake maganganu.

Dan siyasar ya na ta tofa albarkacin bakinsa yayin da Muhammadu Sanusi II ya dawo karagar mulki a matsayin sarki daya tilo a Kano.

Muhammadu Sanusi II
Gwamnati ta dawo da Muhammadu Sanusi II sarautar Kano Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Muhammadu Sanusi II: Siyasa ko kaddara?

Kara karanta wannan

Muhammadu Sanusi II: Abubuwa 7 da suka faru a rayuwar Sarki bayan tube shi a 2020

Da yake magana a Facebook ranar Alhamis, Injiniya Muazu Magaji Dansarauniya ya ce siyasa tana tasiri a sha’anin masarautar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dansarauniya ya ankarar da Mai martaba Muhammadu Sanusi II cewa za suyi masa biyayya muddin sarautar shi ya sa a gaba a Kano.

Amma idan sarki zai rika tsoma baki a sha’anin siyasa, tsohon kwamishinan ayyukan ya bayyana cewa za su yi adawa da shi.

"Za mu bi Sarki Sanusi II idan..." - Dan Sarauniya

"Mulki na Allah ne!"
"Idan Muhammadu Sanusi II Sarauta ya dawo yayi, to mu dama ita ta haife mu, muna masu biyayya!"
"Idan kuma Siyasa ya dawo yayi to mu a cikin ta ya samemu, muna adawa!"

'Dan APC ya yi kira ga Sarakan Kano

Kafin nan an ji ‘dan siyasar yana ba da shawara ga sarakunan da aka sauke da su shirya ba da gudumuwa idan an fito yakin zabe a 2027.

Kara karanta wannan

"Zan yi bincike," Kwankwaso ya yi magana kan mayar da Sarki Sanusi II kan mulki

“Duk mai son yayi Sarki a gidan Dabo shima ya fito hoha ya taya mu kamfen a 2027! Faqat!”

- Muazu Magaji

Jagoran tafiyar Win Win a siyasar Kano yana zargin cewa katsalandan da fada ta rika yi a siyasa ya haifar mata da matsala.

"Mu gaya wa kanmu gaskiya!"
"Hada Sarauta da Siyasa ne asalin ruguza Martabar Masarauta a Kano."

- Muazu Magaji

Kwankwaso da yadda Sanusi II ya dawo

Ana da labari Rabiu Kwankwaso ya ce idan ya zo Kano, zai nemi bayanin yadda gwamnatin Abba Yusuf ta taba masarautu ba.

Rabiu Kwankwaso ya ce ba shi ya sa Abba ya sake naɗa Muhammadu Sanusi II ba amma zai bincika domin fahimtar abin da ya faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel