Kano: Sojoji Sun Ja Daga Yayin da Abba Kabir Ya Umarci Cafke Aminu Ado Bayero

Kano: Sojoji Sun Ja Daga Yayin da Abba Kabir Ya Umarci Cafke Aminu Ado Bayero

  • An sake turo jami'an sojoji da za su ci gaba da kare tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero bayan umarnin kama shi daga Gwamna Abba Kabir
  • Gwamnan ya bada umarnin ne bayan zargin tsohon Sarkin da neman ta da hankulan mutane a jihar bayan tube shi daga sarautar jihar
  • Wannan na zuwa ne bayan sake dawowar Aminu Ado Bayero cikin Kano da asubahin yau Asabar da misalin karfe 4:30 domin shigowa fadarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Dakarun sojoji sun ba tsohon Sarki Aminu Ado Bayero kariya a Kano bayan tube shi a sarauta.

Daukar matakin ya biyo bayan umarnin Gwamna Abba Kabir na cafke tsohon sarkin da ya shigo garin Kano.

Kara karanta wannan

Rudani yayin da tsohon Sarki Aminu Ado Bayero ya koma fada a Kano, bidiyo ya fito

An jibge dakarun sojoji domin ba Aminu Ado kariya
Bayan umarnin Abba Kabir, an sake karo jami'an sojoji domin kare Aminu Ado Bayero. Hoto: Aminu Ado Bayero, Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Sojoji sun ba da kariya ga Aminu Ado

Daily Trust ta tattaro cewa sojoji sun mamaye fadarsa da ke Nasarawa bayan umarnin gwamnan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da sojoji ne suka rako tsohon sarkin zuwa Kano daga filin jirgi sama, har yanzu ba a san mene dalilin sake karo jami'an ba.

Wannan na zuwa ne bayan Aminu Ado Bayero ya shigo garin Kano da karfe 4:30 na asuba inda ya gabatar da salla a cikin filin jirgi.

Aminu Ado ya samu tarba daga jama'a

Shigowar tsohon Sarkin ke da wuya ya samu tarba daga dubban jama'a da suke jan ayoyi daga Suratul Fatihah.

"Kai kadai muke bautawa kuma a gare ka kadai muke neman taimako."

- Dubban masoyan Ado Bayero

Yayin da wasu ke cewa Allah ya kashe dukkan makiyan Aminu Ado Bayero.

Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin hadimin Shugaba Bola Tinubu a bangaren tsaro, Nuhu Ribadu shi ya ba da umarni a dawo da Aminu Ado kan kujerar sarauta.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya ɗauki zafi, ya ba da umarnin a kama tsohon Sarkin Kano

Abba ya umarci kama tsohon sarkin Kano

Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin a kama tsohon sarkin Kano, Aminu Ado Bayero cikin gaggawa.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar da sanyin safiyar yau Asabar, 25 ga watan Mayu.

Gwamna Abba Kabir ya zargi tsohon sarkin da aka tsige da yunƙurin ta da zaune tsaye da haifar da tashin hankali a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel