Majalisar dattawan Najeriya
An fara gudanar da taron jin ra'ayoyin jama'a kan kasafin kudin 2024 da shugaban kasa Tinubu ya gabatarwa majalisar dokokin tarayya a birnin tarayya Abuja.
Sanata Ali Ndume, daga jihar Borno ya kwatanta gwamnatin tsohon Shugaba Buhari da ta Bola Tinubu mai ci yanzu, ya ce Tinubu ya kaucewa kura-kuren Buhari.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswilƙ Akpabio, ya ce ya kamata Kudu maso Kudancin Najeriya su saka wa shugaban kasa, Bola Tinubu ta hanyar zaben APC.
Dan majalisar tarayya, Alhassan Doguwa, ya karyata ikirarin cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatarwa yan majalisa da fankon kasafin kudin shekara mai zuwa.
Yan Najeriya sun yi martani bayan kotu ta yanke hukunci kan shari'ar gwamnatin jihar Kano da Alhassan Ado Doguwa wanda ake zargi da kisan kai a lokacin zaben 2023.
Babbar kotun Tarayya ta yi fatali da korafin Gwamna Abba Kabir kan zargin ta'addanci da ya ke yi wa Alhassan Ado Doguwa, ta umarce shi ya biya Ado diyyar miliyan 25.
Wasu `yan majalisar tarayya su na zargin cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya yaudare su inda suka ce ya mika musu kundin kudurin kasafin kudin 2024 na bogi.
Majalisar Dattawa ta bukaci Shugaba Tinubu da ya dakatar da tura kudaden kananan hukumomin da babu zababbun shugabanni a jihohi 16 da ke fadin kasar.
Majalisar dattawa ta ce bincikenta ya nuna mata an karkatar da kudin tallafin da bankin CBN ya ba kamfanoni. Biliyoyin da CBN ya ba kamfanonin mai sun bi iska.
Majalisar dattawan Najeriya
Samu kari