Kotun Daukaka Kara Ta Rusa Zaben Sanatan LP, Ta Bayyana Sahihin Wanda Ya Lashe Zabe

Kotun Daukaka Kara Ta Rusa Zaben Sanatan LP, Ta Bayyana Sahihin Wanda Ya Lashe Zabe

  • Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari’ar zaben Majalisar Tarayya ta Abia ta Tsakiya a yau Asabar
  • Kotun, yayin hukuncin nata ta kwace kujerar Sanata Darlington Nwokocha na jam’iyyar LP
  • Har ila yau, kotun ta ayyana Kanal Austin Akobundu na jam’iyyar adawa ta PDP a matsayin wanda ya lashe zabe

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Abia – Kotun daukaka kara ta kwace kujerar sanatan Abia ta Tsakiya, Darlington Nwokocha na jam’iyyar LP.

Kotun har ila yau, ta ayyana dan takarar jam’iyyar PDP, Kanal Austin Akobundu a matsayin wanda ya lashe zaben, Legit ta tattaro.

Kotun zabe ta rusa zaben sanata a Abia, ta fadi wanda ya yi nasara
Kotun Daukaka Kara Ta Rusa Zaben Sanatan LP, a Abia. Hoto: PDP Nigeria.
Asali: Facebook

Mene PDP ke cewa kan hukuncin kotun?

Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ita ta bayyana haka a shafinta na Twitter a yammacin yau Asabar 4 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Zaben Kogi: Kungiya ta nemi a kama Dino Melaye kan dalili 1 tak, ta yi bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyar ta ce Kanal Akobundu na Abia ta Tsakiya da Sanata Osita Ngwu na Enugu ta Yamma su ne kadai sanatocin jam’iyyar daga Kudu maso Gabashin kasar.

Wannan hukuncin kotun na tabbatar da cewa Sanata Darlington Nwokocha zai bar kujerarshi ta sanata ga Akobundu.

Wane martani sanatan ya yi?

Kanal Akobundu ya godewa jama'a kan irin goyon bayan da su ke ba shi inda ya ce wannan nasara ta al'ummar yankin ne.

Akonondu ya bayyana haka ne ta bakin hadiminsa, Uche Nwosi a yau Asabar 4 ga watan Nuwamba bayan hukuncin zaben.

Bayan godiya ga jama'ar yankin, ya kuma godewa bangaren shari'a kan irin wannan hukuncin adalci.

Ya ce Wannan nasara ba ta shi ba ce, dimukradiyya ce ta yi nasara a wannan hukuncin kotun.

Kotun daukaka ta yi hukunci kan shari'ar Kingibe

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta tabbatar da zaben jihar Arewa wanda bai kammala ba, ta ba da sabon umarni

A wani labarin, kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Sanata Ireti Kingibe a matsayin wacce ta lashe zaben sanatar Abuja.

Kingibe, wacce 'yar jam'iyyar LP ce ta yi nasara kan dan takarar jam'iyyar PDP, Philip Aduda daya shafe shekaru kan kujerar.

Kotun, yayin hukuncin, ta yi fatali da korafe-korafen Aduda inda ta ce ba shi da gamsassun hujjoji na wargaza zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel