Majalisar dattawan Najeriya
Dakatattun 'yan majalisar dokokin jihar Zamfara guda takwas, da aka dakatar sun shigar da kara a gaban kotu, kan kakakin majalisar da wasu mutum shida.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa ta iya yiwuwa wasu sojojin haya daga kasar waje ne suka shigo suka kashe sojoji 17.
Yayin da aka dakatar da Sanata Abdul Ningi kan zargin cushe a kasafin kudin shekarar 2024, akwai yiwuwar sanatan zai koma kujerarsa yayin ake tattaunawa.
Musa Iliyasu Kwankwaso babban jigo a jam'iyyar APC ta jihar Kano, ya bukace 'yan majalisun Arewa da kada su bari zargin cushe a kasafin kudi ya raba kansu.
Ned Nwoko, sanata mai wakiltar Delta ta Arewa, ya bayyana cewa ya samu kudin ayyukan mazaba da suka kai Naira biliyan daga kasafin kudin da aka raba wa 'yan majalisu
Majalisar dattawa ta yi martani kan kisan gillar da aka yi wa jami'an sojoji 16 a jihar Delta. Majalisar ta bukaci a tabbatar da cewa maharan sun fuskanci hukunci.
Wasu sun fito sun soki yadda aka yi wuf aka dakatar da Abdul Ningi daga majalisa. Kungiyar Arewa ta bukaci Majalisa ta soke dakatarwar Sanata Abdul Ningi.
Duk da cewa babu wata doka a Najeriya da ta hana tsofaffin gwamnoni neman zama sanatoci, amma manazarta na ganin kamar sun mayar da abun al'adar su.
Bayan Sanata Abdul Ningi ya miƙa takardar murabus, NSF ta naɗa Sanata Abdul'azizi Musa Ƴar'adua a matsayin sabon shugaban sanatocin arewacin Najeriya.
Majalisar dattawan Najeriya
Samu kari