Majalisar Dattawa Ta Titsiye Manyan Hafsoshin Tsaron Ƙasa, Bayanai Sun Fito

Majalisar Dattawa Ta Titsiye Manyan Hafsoshin Tsaron Ƙasa, Bayanai Sun Fito

  • Rahotanni sun nuna cewa manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan sun bayyana gaban majalisar dattawa yau Laraba
  • Majalisar ta gayyace su ne domin su mata bayani kan yanayin tsaro da ke ƙara lalacewa da halin da ake ciki a birnin Abuja
  • Wannan na zuwa ne yayin da sha'anin tsaro ya tabarbare a birnin tarayya da kuma kisan sarakuna 2 a Ekiti wanda ya ja hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta titsiye manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan kan taɓarɓarewar tsaro a sassan Najeriya a cikin ƴan makonnin nan.

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, majalisar ta jingine dokar hana bakin fuska shigowa domin baiwa hafsoshin tsaro da hadimin shugaban ƙasa damar yin bayani.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Birnin tarayya Abuja na fuskantar babbar barazana, majalisar dattawa ta magantu

Majalisar dattawan Najeriya.
Majalisar Dattawa Ta Titsiye Manyan Hafsoshin Tsaron Ƙasa, Bayanai Sun Fito Hoto: Senate
Asali: UGC

Mai bai wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, shawara kan harkokin majalisa, Sanata Abdullahi Gumel da hafsoshin tsaron ne suka bayyana domin yi wa sanatoci ƙarin haske.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan ƙusoshin zasu yi wa majalisar dattawa jawabi ne kan halin rashin tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa a faɗin ƙasar nan.

Domin samar da mafita mai ɗorewa, ana kuma sa ran shugabannin hukumomin tsaron za su yi wa zauren bayani kan ayyukan ƴan bindiga da garkuwa da mutane a birnin tarayya.

Majalisa ta ɗage sauraron hafsoshin

Channels tv ta tataro cewa majalisar dattawa ba ta samu tattaunawa da hafsoshin tsaron ba kamar yadda aka tsara saboda rashin halartar mai bada shawara kan tsaro, Nuhu Rubadu.

Jim kaɗan bayan an ba su damae shiga zauren, hafsoshin tsaron sun fito sun koma wuraren aikinsu sakamakon ɗage zaman da majalusar ta yi zuwa makon gobe.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Majalisar dattawa ta yi amai ta lashe, ta aike da saƙo ga NSA da wasu ministoci 3

Shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio yayin da yake amincewa da dage zaman, ya bayyana cewa majalisar za ta so yin cikakken nazari kan rashin tsaron da ake fama da shi.

Majalisa za ta gyara kundin zaben 2022

A wani rahoton na daban Kudirin sake garambawul a kundin dokokin zaben Najeriya 2022 ya tsallaka zuwa karatu na biyu a majalisar wakilan tarayya.

Majalisar ta amince da kudirin a zaman ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, 2024 bayan ɗan majalisa daga jihar Delta ya gabatar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel