Fadar shugaban kasa
Gwamnan jihar Benuwai, Hyacinth Alia, ya gana da mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, a Aso Villa kan batun samar da wadataccen abinci a ƙasa.
Ƙungiyar fulani makiyaya ta ƙasa (MACBAN) ta yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa yayanta a muƙaman gwamnati ko da kuwa na shara ne a Aso Villa.
Yayin da aka fara zanga-zanga a faɗin Najeriya, Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sa labule da shugabannin ƙungiyoyin kwadago na ƙasa a fadarsa Aso Villa.
Wasikar Bola Ahmed Tinubu za ta isa teburin shugaban Majalisar dattawa a yau. Ana shirye-shiryen tura sunayen sahu na biyu na mutanen da ake so su zama Minista.
Kungiyar kwadugo ta ƙasa NLC ta ce zata sake komawa da mutanen da take wakilta su kara tattauna wa domin ɗaukar matsaya kan zanga-zangar da za a fara gobe.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dawo Najeriya bayan kai ziyara Jamhuriyar Benin a yau don halartar taron murnar zagayowar samun 'yancin kasar karo na 63.
Majalisar dattawa za ta kammala tantance ministocin da Shugaba Tinubu ya naɗa a yau Talata. Majalisar za ta tantance ragowar ministocin su 14 a yau Talata.
An gayyaci Bola Ahmed Tinubu zuwa bikin taya Benin cika shekara 63 da ‘yancin kai. Gwamna Dapo Abiodun, Babajide Sanwo-Olu, Seyi Makinde za su yi masa rakiya.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta tattala makudan kudin da suka kai naira tiriliyan ɗaya daga cire tallafin kan fetur a Najeriya.
Fadar shugaban kasa
Samu kari