Tashin Hankali Yayin da Ake Shirin Tsige Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu

Tashin Hankali Yayin da Ake Shirin Tsige Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu

  • Ana cikin zaman dar-dar a jihar Ondo yayin da ake sa ran majalisar dokokin jihar za ta tsige gwamnan na yanzu Rotimi Akeredolu
  • A ranar Lahadi shugaban kasa Tinubu ya bukaci 'yan siyasar jihar da su wanzar da zaman lafiya ba tare da an cire kowa daga mukaminsa ba
  • Sai dai wani dan majalisa ya ce akwai yiyuwar tsige Akeredolu a zaman majalisar na gobe tare da ayyana Aiyedatiwa mukaddashin gwamna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Ondo - Akwai tashin hankali yayin da 'yan majalisun Ondo za su gudanar da zamansu na farko a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba bayan ganawa da Shugaba Tinubu kan rikicin siyasar jihar.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan PDP ya daga wa mai gidansa yatsa, ya fito takarar gwamna a jihar

An samu rahotanni daban-daban kan abinda zaman ya kunsa, inda magoya bayan mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa, ke son a tabbatar da shi mukaddashin gwamna.

Rotimi Akeredolu/Jihar Ondo
Rahotanni sun bayyana cewa akwai yiyuwar ayyana Aiyedatiwa matsayin mukaddashin gwamna a ranar Talata. Hoto: @RotimiAkeredolu
Asali: Twitter

Tinubu ya sa baki kan rikicin jihar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya daga makusantan Gmamna Oluwarotimi Akeredolu ya ce akwai shirin da aka gano an kulla da Tinubu na tsige shi daga gwamna tare da maye gurbinsa da Aiyedatiwa.

Hadimin Shugaba Tinubu ta fuskar watsa labarai, Ajuri Ngelale, a cikin wata sanarwa da ya fitar bayan taron, ya ce Shugaba Tinubu ya nemi a sasanta rikicin.

"Hakan na nufin Akeredolu ya ci gaba da zama matsayin gwamnan jihar, Aiyedatiwa mataimaki, yayin da kowanne dan majalisa da shugwabannin majalisar su ci gaba da aikinsu ba canji."

Me ya jawo tashin hankali a jihar?

A cewar wani rahoto, an samu wasu 'yan majalisu goma sha daya da ke goyon bayan Aiyedatiwa na da shirin janyo magoya bayan Akeredolu zuwa bangarensu, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Wani Gwamnan ya sake fallasa yadda aka kai Najeriya gargara kafin zuwan Tinubu

Daya daga cikin 'yan majalisar wanda aka tuntuba daren jiya bayan dawowa daga Abuja ya ce akwai yiyuwar ayyana Aiyedatiwa matsayin mukaddashin gwamna a ranar Talata.

Shugaban jam'iyyar na jihar, Hon. Ade Adetimehin, ya ce babu wani dan siyasa a jihar da zai yi jayayya da matsayar da Shugaba Tinubu ya cimmawa kan rikicin jihar.

The Guardian ta ruwaito yadda magoya bayan 'yan siyasar biyu suka yi shirin gudanar da babbar zanga-zanga a jihar Ondo, lamarin da ya kara rura wutar rikicin.

Dan majalisar Kano ya shirya addu'a ta musamman ga Tinubu

A wani labarin, wani mamba a majalisar wakilan tarayya, Abdulmumin Jibrin, ya gudanar da taron addu'o'i ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, rahoton Legit Hausa.

Jibrin wanda jigo ne a jam'iyyar NNPP, ya tara malamai don yin addu'a ga uban gidansa, Rabiu Kwankwaso, da kuma gwamnan Kano, Abba Kabir.

Asali: Legit.ng

Online view pixel