Labari Da Dumi Dumi: Tinubu Zai Gabatarwa 'Yan Majalisa Kasafin Kudin Farko a Mulkinsa

Labari Da Dumi Dumi: Tinubu Zai Gabatarwa 'Yan Majalisa Kasafin Kudin Farko a Mulkinsa

  • Bola Ahmed Tinubu ya shirya domin ya gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa a zauren majalisar tarayya
  • A bisa al’ada, Shugaban kasa ya na kai kundin kasafin kudi ne gaban Sanatoci da ‘Yan majalisar wakilai na kasa
  • Akwai yiwuwar a kasafin kudin farko da Tinubu ya shirya, gwamnatin tarayya ta kashe kusan Naira tiriliyan 26

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da kundin kasafin kudin shekara ta 2024 a gaban ‘yan majalisar tarayya.

Rahoton da aka samu daga gidan talabijin Channels ya ce za a gabatar da kasafin kudin ne a ranar Larabar nan.

Sakataren bincike da yada labarai a majalisar tarayya, Dr. Ali Barde Umoru ya tabbatar da haka a yammacin yau.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ake shirin tsige Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu

BolaTinubu
Shugaba BolaTinubu ya shirya kasafin kudi Hoto; Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu zai isa Majalisa a ranar Laraba

Dr. Ali Barde Umoru ya shaidawa manema labarai haka yayin da yake amsa tambayoyi.

Jami’in majalisar tarayyan ya bukaci gidajen jaridu su aiko sunayen wadanda za a ba izinin shigowa zauren a ranar.

...MTFE da FSP

Kafin a kai ga haka, rahoton ya ce fadar shugaban kasa ta aikawa Sanatoci da ‘yan majalisar tarayya MTFE da FSP.

Bayanan da ke cikin tsarin kashe kudin ya nuna gwamnati ta yanke shawarar batar da N26.1tr a shekarar 2024 mai zuwa.

Kwamitin tattalin arziki da kudi na majalisar dattawa ya yi zama da jami’an gwamnati wajen amincewa da MTEF.

Abin da kasafin kudin Tinubu zai kunsa

Punch ta ce ‘yan majalisn sun amince a karbo bashin N7.8tr a kasafin kudi na badi.

Baya ga haka, an tsaida farashin gangar mai a kan $73.96 da lissafin cewa za a rika hako ganguna miliyan 1.78 a rana.

Kara karanta wannan

Sheikh Bala Lau ya yabawa Uba Sani kan 'inganta walwalar' mazauna Kaduna

Wannan ne karon farko da Mai girma Bola Tinubu zai gabatar da kasafin kudi bayan ya canji Muhammadu Buhari.

Shugaba Bola Tinubu ya yi nadin mukamai

Tsohon Mai ba Ministan kasafin kudi shawara, Armstrong Takang Ph.D. zai cigaba da rike MOFI kamar yadda aka ji labari.

Dr. Shamsudeen Usman wanda ya yi Minista a lokacin ‘Yaradua da Jonathan ya rike matsayinsa na mai sa ido a kamfanin.

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin shugabannin kamfanin na MOFI ne bayan dawowa daga kasar waje kwanaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel