Gasar kwallo
Wani ‘dan Najeriya wanda ya yi hasashen sakamakon AFCON a matakin rukuni, ya yi hasashen cewa Najeriya za ta yi nasara kan Ivory Coast a wasan karshe.
Fasto Dakta Kan Ebube Muonso ya yi hasashen kasar da za ta lashe gasar AFCON a gobe Lahadi 11 ga watan Faburairu inda ya ce Ivory Coast ce da nasara.
Wani ‘dan Najeriya ya ce zai fi kyautuwa mutum ya guji kallon wasan Najeriya da Ivory Coast idan har ya san yana da hawan jini. Ya ce zai fi kyau a bi sakamakon.
A yayin karo tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu a wasan kusa da karshe na gasar cin kofin Afrika, AFCON, akalla ‘yan Najeriya biyar ne suka mutu saboda zullumi.
Ahmed Musa ya jagoranci tawagar Super Eagles wurin yin addu'a na musamman ga wadanda suka rasa ransu yayin kallon wasanta da Afirka ta Kudu a ranar Laraba.
Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya tuna haduwarsa da wani dan Obidient a yayin wasan Najeriya da Afrika ta Kudu.
Wani ɗan kasuwa ya rasa rayuwarsa a lokacin da alƙalin wasa ya kashe kwallon da Osimhen ya zura a wasan Super Eagles da South Africa a gasar cin kofin AFCON.
Magoya bayan Afirka ta Kudu sun gargadi golan Najeriya, Stanley Nwabali kan komawa kasar don ci gaba da buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Chippa United.
Mataimakin Bursar na jami’ar Kwara, Alhaji Ayuba Abdullahi, ya rasu a lokacin da yake kallon wasan kusa da na karshe tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu.
Gasar kwallo
Samu kari