Fitaccen 'Dan Wasan Real Madrid, Toni Kroos, Zai Yi Ritaya Daga Buga Kwallon Kafa

Fitaccen 'Dan Wasan Real Madrid, Toni Kroos, Zai Yi Ritaya Daga Buga Kwallon Kafa

  • Fitaccen dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Toni Kroos ya bayyana cewa zai yi ritaya daga buga kwallon kafa
  • Kamar yadda ya bayyana a yau Talata, Toni Kroos ya ce zai ajiye takalmansa ne da zarar an kammala gasar Euro 2024 a kasar Jamus
  • Fitaccen dan wasan zai cika burinsa na yin ritaya a Real Madrid kuma a daidai lokacin da ya ke cikin kololuwar ganiyarsa a kwallo

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

'Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Toni Kroos, ya bayyana cewa zai yi ritaya daga buga kwallo bayan kammala gasar Euro 2024 a kasar Jamus.

A farkon wannan watan ne aka ruwaito Kroos na daf da amincewa da tsawaita kwantiraginsa da Madrid, wanda zai sa ya ci gaba da zama a Santiago Bernabeu a kakar wasa ta 2024-25.

Kara karanta wannan

TotalEnergies ya juyawa Najeriya baya kan aikin dala biliyan 6, an zabi kasar Angola

Toni Kroos ya yi magana kan yin ritaya daga kwallon kafa
Dan wasan Real Madrid, Toni Kroos, ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa. Hoto: @ToniKroos
Asali: Twitter

Sai dai a yau Talata, Kroos ya tabbatar da hukuncin da ya yanke na ajiye takalminsa a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Real Madrid: Sanarwar Toni Kroos

'Dan wasan na tsakiya, ya bayyana cewa:

"Ranar 17 ga Yuli, 2014 na gabatar da kaina a Real Madrid, ranar da ta canza rayuwata a matsayin dan kwallon kafa. Kuma ranar ta bude sabon babi na rayuwata a babban kulob na duniya.
"Sai dai bayan shekaru 10, wannan babin zai zo ƙarshe idan aka kammala wannan kakar ta bana. Ba zan taba mantawa da wannan lokacin mai cike da nasara ba!
"Ina so in gode wa kowa da kowa musamman masoya na 'yan Madrid, saboda ƙaunar da kuka nuna mun tun daga ranar farko har zuwa ta ƙarshe."

Kroos ya yi ritaya daga kwallo

Kara karanta wannan

2023/2024: Man City ta lashe gasar Premier, ta kafa tarihi a duniyar kwallon kafa

Fitaccen dan wasan Madrid ya ci gaba da cewa:

"A lokaci guda kuma, wannan matakin da na dauka yana nufin cewa zan yi ritaya daga buga kwallon kafa a wannan bazarar bayan an kammala gasar Euro.
"Kamar yadda na saba cewa: Real Madrid ce kungiyar kwallon kafa ta karshe da zan buga ma wasa. Ina farin ciki da alfaharin cewa na yanke wannan hukuncin a lokacin da ya dace.
"Babban burina a koyaushe shi ne in yi ritaya daga buga kwallon kafa a lokacin da na ke matakin kololuwar ganiyata."

Karanta sanarwar a nan kasa:

Ronaldo: Dan wasa mafi albashi a duniya

A wani labarin, mun ruwaito cewa an ayyana fitaccen dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo, a matsayin dan wasa mafi samun albashi a duniya a 2024.

Wannan kuwa na zuwa ne bayan da Ronaldo ya ke rike da wannan kambu tun daga 2020 har zuwa yanzu, inda ya samu dala miliyan 260 a matsayin albashi a wannan shekarar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.