Ronaldo Ya Fashe da Kuka Yayin da Al Nassr Ta Yi Rashin Nasara a Gasar Cin ‘Kofin Sarki’

Ronaldo Ya Fashe da Kuka Yayin da Al Nassr Ta Yi Rashin Nasara a Gasar Cin ‘Kofin Sarki’

  • Cristiano Ronaldo ya zubar da hawaye bayan da kungiyarsa ta Al Nassr ta sha kashi a hannun Al Hilal a bugun fanariti a gasar cin kofin sarki
  • Fitaccen dan wasan na Portugal, wanda ya zura kwallaye 58 a wasanni 64 a kungiyar Al-Nassr ya zube kasa a lokacin da Al Hilal ke murna
  • Al-Hilal ta yi nasara da ci 5-4 a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da aka tashi wasan farko da kunnen doki har zuwa karin lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jeddah, Saudiya - Cristiano Ronaldo ya zubar da hawaye bayan da kungiyarsa ta Al-Nassr ta sha kashi a hannun abokiyar hamayyarta Al-Hilal a ranar Juma'a da daddare a wasan karshe na cin 'kofin sarki'.

Kara karanta wannan

Harin masallacin Kano: Za a fara shari’ar matashin da ya kona mutane da asuba

Ronaldo ya zubar da hawaye bayan faduwar a gasar cin 'kofin sarki'
Saudiya: Ronaldo ya yi hawaye bayan faduwar Al Nassr a gasar cin 'kofin sarki'. Hoto: @baytAlhilal
Asali: Twitter

Tsohon dan wasan na Manchester United ya durkushe a kan guiwowinsa bayan da ‘yan wasa tara na Al-Hilal suka yi nasara da ci 5-4 a bugun daga kai sai mai tsaron gida a Jeddah.

Al-Nassr ba ta daga kofi a bana ba

An lallashi dan wasan mai shekaru 39, wanda ya kafa sabon tarihin zura kwallo a gasar 'Saudi Pro League' da kwallaye 35, in da aka fitar da shi daga filin yana kuka, in ji rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kyaftin din Portugal ya zura kwallaye 58 a wasanni 64 a kungiyar Al-Nassr tun bayan da ya koma kungiyar a watan Janairun 2023 bayan da ya bar United.

Kungiyar Al-Nassr ta tashi tutar babu a wannan kakar ba tare da wani kofi ba, amma a bara Ronaldo ya tsira da sarkar azurfa daya tilo a gasar cin kofin zakarun Larabawa.

Kara karanta wannan

Wa zai zama Sarkin Kano? Abin da kotuna 2 suka ce game da makomar Sanusi II da Aminu

Al-Nassr ta sha kashi hannun Al-Hilal

Channels TV ta ruwaito Al Nassr da Al-Hilal sun yi kunnen doki har bayan da aka kammala zagayen karin lokaci, lamarin da ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Bayan da tsohon dan wasan Wolves, Ruben Neves ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron gidan Al-Hilal, shi ma tsohon dan wasan bayan United, Alex Telle ya kasa zura kwallon.

Kungiyoyin biyu sun ci bugun finareti hudu, ciki har da bugun Ronaldo, kafin mai tsaron gidan Al Hila, Yassine Bounou ya buge kwallon karshe da dan wasan Al-Nassr ya buga wanda ya ba Al-Hilal nasara.

Kalli bidiyon Ronaldo na kuka, wanda @UTDTrey ya wallafa a shafinsa na X.

Barcelona ta sallami kocinta Xavi Hernández

A wani labarin, mun ruwaito cewa FC Barcelona da Xavi Hernández Creus sun kawo karshen kwantiragin da ke tsakaninsu, inda kun giyar ta sallame shi da sauran tawagarsa.

Xavi, wanda ya buga wa Barça wasanni sama da 700 a matsayin dan wasa, ya karbi ragamar horar da kungiyar a shekarar 2021 kuma ya taimaka kungiyar ta daga kofi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel