Hukumar yan sandan NAjeriya
Wani jami'in ɗan sanda ya shiga hannun hukuma bayan ya yi yunƙurin halaka abokin aikins a jihar Kaduna. Ɗan sandan dai ya shaƙe abokin aikin nasa ne da igiya.
Gungun matasa wadanda suka fusata sun cika titunan birnin Kano don nuna damuwarsu da kin jinin rushe-rushe da gwamnatin Abba Gida Gida jihar ke yi a kullum.
Wasu 'yan bindiga ɗauke da manyan makamai sun halaka shugaban 'yan banga a ƙaramar hukumar Danmusa da ke jihar Katsina, a yayin wani farmaki da suka kai a.
Al'ummar Hausawa da ke karamar hukumar Takum a jihar Taraba sun zargi kabilar Kuteb da kashe musu mutane 32 inda suka bukaci mahukunta su dauki mataki akansu.
Wani matashi mai suna Usman Buda mahauci ya rasa ransa bayan wasu fusatattun matasa sun kaishi lahira bisa zargin batanci ga annabi Muhammad a jihar Sokoto.
Tsohon kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, Frank Odita ya yi bankwana da duniya yana da shekara 84. Odita ya koma ga mahaliccinsa ne bayan gajeruwar jinya.
Gwamnan jihar Filato, Celeb Mutfwang, ya bayyana cewa yana da kwarin guiwar sabbin hafsoshin tsaron da aka naɗa zasu taka rawa wajen magance kalubalen tsaro.
Wasu 'yan bindiga da ba'a iya tantance ko su waye ba sun kashe aƙalla mutane uku, tare da jikkata wasu biyu, a wani mummunan hari da suka kai a jihar Filato.
Rundunar 'yan sanda sun bazama neman matashi mai suna Ankush Dutta bayan shafe shekaru biyu a dakin otal bai biya ko sisi ba, an kiyasta bashin ya kai N57m.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari