Sabbin Hafsoshin Tsaro da IGP Zasu Dawo da Zaman Lafiya a Filato, Mutfwang

Sabbin Hafsoshin Tsaro da IGP Zasu Dawo da Zaman Lafiya a Filato, Mutfwang

  • Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya taya sabbin hafsoshin tsaron Najeriya da sifetan yan sanda na kasa murna
  • Ya ce yana da yaƙinin cewa suna da gogewar da zasu iya magance matsalar tsaron da ta addabi jihar Filato da Najeriya baki ɗaya
  • Mutfwang ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya yi zaɓi nagari domin ya zakulo zakaƙuran mutanen da suka cancanta

Plateau - Gwamnan jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang, ya bayyana kwarin guiwar cewa sabbin hafsoshin tsaro da muƙaddashin sifetan 'yan sanda zasu taka rawa wajen dakile taɓarɓarewar tsaro.

Gwamnan ya nuna yaƙinin cewa sabbin hafsoshin, waɗanda suka karɓi ragama zasu iya kawo karshen ayyukan ta'addanci a wasu sassan ƙasar nan, musamman a Filato.

Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato.
Sabbin Hafsoshin Tsaro da IGP Zasu Dawo da Zaman Lafiya a Filato, Mutfwang Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Mutfwang ya faɗi haka ne a wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran ofishin gwamnan Filato, Gyang Bere, ya raba wa manema labarai a Jos, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Nuna Takaicinsa Kan Kisan Manoma a Borno, Ya Bayyana Kwakkwaran Matakin Da Zai Dauka

Ya ce naɗin hafsoshin tsaron da shugaba Tinubu ya yi a kwanan nan ya zo a kan gaɓa daidai lokacin da 'yan ta'adda ke barazana ga tsayuwar kasar nan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta shirya tsaf zata yi aiki kafaɗa da kafaɗa da hafsoshin tsaro da sauran kayan samar da tsaro daga tarayya domin kawo karshen zubda jini.

Shugaba Tinubu ya zaɓi mutanen da suka cancanta

Gwamna Mutfwang ya kuma ayyana sabbin hafsoshin tsaron a matsayin mutanen da suka yi matuƙar cancanta, masu kwarewa da hangen nesa kuma jajirtattu.

Mai girma gwamnan Filato ya ce ya yi imanin zasu baje kolin gogewarsu da sanin makamar aiki wajen daƙile dukkanin kalubalen tsaron da suka addabi Najeriya.

Gwamna ya aike da saƙon taya murna ga sabbin hafsoshin tsaron

Gwamnan ya taya sabbin hafsoshin tsaron murnar taka wannan matsayi kana ya yi Addu'ar Allah ya ƙara musu karfin guiwar shawo kan matsalar tsaro a Filato da Najeriya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Zulum Ya Sha Alwashin Daukan Mataki Kan Kisar Gillar Mutum 8 Da ISWAP Ta Yi A Borno

A cewarsa, ta haka ne kaɗai 'yan Najeriya zasu samu sa'ida bayan samun tabbacin tsaro da kariya.

Shugaba Tinubu Ya Faɗi Gaskiyar Yadda Ya Cire Tallafin Man Fetur Ranar Rantsarwa

A wani rahoton na daban shugaban kasa ya bayyana yadda ya faɗi cewa tallafin mai ya tafi duk babu batun a cikin jawabinsa na ranar rantsarwa.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce waɗanda suka shirya masa jawabin ranar bikin rantsuwar kama aiki ba su sanya batun cire tallafin mai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel