Kotun Shari'ar Musulunci A Kano Ta Daure Lauyan Bogi Watanni 15 A Gidan Kaso

Kotun Shari'ar Musulunci A Kano Ta Daure Lauyan Bogi Watanni 15 A Gidan Kaso

  • Kotun Shari'ar Musulunci da ke karamar hukumar Kiru ta jihar Kano ta daure lauyan bogi watanni 15 a gidan kaso
  • Wanda ake zargin mai suna Zaharaddin Sani Maidoki ya amsa dukkan tuhume-tuhumen da aka zayyana masa
  • Alkalin kotun, Abdulmuminu Gwarzo ya daure shi watanni 15 a gidan kaso tare da biyan makudan kudade har N20,000

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - An gurfanar da wani lauyan bogi mai suna Zaharaddin Sani Maidoki a gaban kotun shari'ar Musulunci bisa zargin yaudara da cin amana.

Kotun da ke zamanta a karamar hukumar Kiru da ke jihar Kano ta daure wanda ake zargin watanni 15 a gidan kaso.

Kotun Shari'ar Musulunci ta daure lauyan bogi a Kano watanni 15
Kotu A Najeriya. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Kotun da ke Kano ta yanke wa lauyan bogin watanni 15 a gidan kaso

Wanda ake zargin wanda dan asalin jihar Kaduna ne ya bayyana kansa a matsayin lauya da niyyar kare wasu mutane a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Al'ummar Hausawan Taraba Sun Nemi Gwamnati Ta Dauki Mataki Kan Kashe Masu Mutane 32 Da Aka Yi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Zaharaddin ya amsa dukkan tuhume-tuhumen da ake kararsa akai wanda ya hada da bayyana kansa a matsayin dan jarida daga jihar Kaduna.

Alkalin kotun, Abdulmuminu Nuhu ya daure wanda ake zargin watanni 15 a gidan gyaran hali, Aminiya ta tattaro.

Hukuncin da Alkalin kotun ya yanke bai ba da damar biyan kudin tara ba, amma zai biya N20,000.

Yayin yanke hukuncin, Alkalin kotun ya daure matashin tare da yin amfani da dokokin shari'a ta jihar Kano karkashin sashe na 337.

Alkalin kotun ya kwace dukkan takardu da katin shaidar aiki

Kotun har ila yau, ta tura sako zuwa Kungiyar Lauyoyi ta jihar Kaduna don tabbatar da ikirarin shi lauya ne, inda kungiyar ta ce ba ta san da zamanshi a kungiyar ba.

Alkalin kotun ya shaida masa cewa yana da kwanaki 30 idan bai gamsu da hukuncin kotun ba zai iya daukaka kara.

Kara karanta wannan

Kano: Dahiru Yellow Ya Shaki Iskar ’Yanci Bayan Shekaru 7 A Gidan Kaso Kan Zargin Safarar ’Yar Bayelsa Tare Da Musuluntar Da Ita

Kotun ta kuma kwace dukkan wasu takardu da ke tare da shi da kuma shaidar katin aiki da yake ikirarin shi lauya ne kuma dan jarida.

Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Kano Daga Rushe Gine-Gine A Jihar

A wani labarin, kotu ta umarci gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya dakatar da rusau da yake yi.

Wannan hukunci na zuwa ne bayan wani mazaunin Kano, Saminu Muhammad ya shigar da gwamnatin kara.

Alkalin kotun, S. A Amobeda a ranar 23 ga watan Yuni ya umarci gwamnan ya dakatar da shirin rushe shaguna a akan hanyar BUK.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel