Rikicin Kabilanci: Hausawa Sun Nemi Abi Musu Kadu, Yayin Da 'Yan Kabilar Kuteb Suka Kashe Musu Mutane 32

Rikicin Kabilanci: Hausawa Sun Nemi Abi Musu Kadu, Yayin Da 'Yan Kabilar Kuteb Suka Kashe Musu Mutane 32

  • Al'ummar Hausawa a karamar hukumar Takum da ke jihar Taraba sun zargi 'yan kabilar Kuteb da kashe musu mutane 32 a yankin
  • Kakakin kungiyar Hausawa a yankin, Sani Abdullahi shi bayyana haka inda ya bukaci mahukunta su dauki mataki
  • Shugaban kabilar Kuteb, Emmanuel Ukwen ya yi fatali da wannan zargi inda ya ce Hausawa suna hada kai da makiyaya don kai musu hari

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Taraba - Al'ummar Hausawa a karamar hukumar Takum da ke jihar Taraba sun bukaci a hukunta 'yan kabilar Kuteb kan zargin kashe musu mutane 32.

Alhaji Sani Abdullahi, kakakin al'ummar Hausawa a yankin shi ya bayyana haka a ranar Lahadi 25 ga watan Yuni a Jalingo babban birnin jihar.

Hausawa suna zargin Kuteb da kashe musu mutane 32 a Taraba
Taswirar Jihar Taraba. Hoto: Punch.
Asali: Facebook

Ya kirayi mahukunta da su binciko tare da hukunta 'yan ta'addan kabilar Kuteb da suka kashe Hausawa da ba su ji ba, ba su gani ba, Daily Trus ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kano: Dahiru Yellow Ya Shaki Iskar ’Yanci Bayan Shekaru 7 A Gidan Kaso Kan Zargin Safarar ’Yar Bayelsa Tare Da Musuluntar Da Ita

Kuteb sun karyata wannan zargi da Hausawa suka yi

Shugaban kungiyar kabilar Kuteb, Emmanuel Ukwen yayin mai da martani yayi watsi da wannan zargi inda ya ce zargin bai da tushe balle makama.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Har ila yau, ya zargi kabilar Hausawa da hada kai da makiyaya wurin kai hari kan 'yan kabilar Kuteb.

Jihar Taraba ta sha fama da rikice-rikice na addini da kabilanci a baya-bayan nan wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyin al'umma a jihar.

Gwamnatoci da dama sun sha alwashin dakile rikicin kabilaci a jihar

Gwamnatoci da dama a jihar sun sha yin alkawarin kawo karshen wadannan tashe-tashen hankula amma abin ya ci tura ganin yadda jihar ke da kabilu daban-daban.

Karamar hukumar Takum na da kabilu daban-daban da ke yawan samun tashe-tashen hankula a tsakaninsu duk da kokarin da masu ruwa da tsaki ke yi don dakile faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Kano: NDLEA Ta Kama Mutum 1,064, Ta Kwace Tan 7.5 Na Miyagun Kwayoyi

Rudani Yayin Da Ake Ta Jin Karan Harbe-harbe Kusa Da Ofishin INEC A Taraba

A wani labarin, an samu rudani a jihar Taraba yayin da ake ta jin harbe-harbe ko ta ina a Jalingo babban birnin jihar.

Wata majiya ta tabbatar cewa harbe-harben na fitowa ne daga ofishin hukumar INEC da kuma Hedkwatar 'yan sanda a yankin.

Majiyar ta tabbatar da cewa ana zargin an samu hatsaniya ne tsakanin jami'an tsaro masu gadin ofishin INEC, inda mutane da dama suka rufe shagunansu da ofisoshi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel