Jihar Niger
Za a ji yadda jami'an tsaron farin kaya na DSS sun yi aikin hadin gwiwa da rundunar sojin Najeriya a kan yan ta'addan da Dogo Gide ya gayyato daga Zamfara zuwa Neja.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya sanar da hana hawan sallah da duk wasu shagulgula domin zaman makoki da alhinin mutanen da suka mutu a ambaliyar Mokwa.
Sanata Abubakar Bello ya ba da N50m ga garin Mokwa da ambaliya ta shafa, yana mai in ta'aziyyar wadanda suka rasu da kuma roƙon Allah ya mayar da asarar da akayi.
Gwamnatin Neja karkashin gwamna Umaru Bago ta bukaci Aliko Dangote ya hada kai da ita domin hako mai a jihar a yankin Bida, Dangote zai zuba jari a Neja.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya girgiza da ambaliyar ruwan da ta kashe sama da mutane 150 a Mokwa a jihar Neja da mutuwar 'yan wasan Kano 22 a hadarin mota
Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Pantami ya mika sakon jaje ga al'ummar Mokwa da ke jihar Neja bisa ambaliyar ruwan da ta afku a yankin da ke jihar Neja.
Rahotanni daga jihar Neja sun tabbatar da cewa tawagar masu aiki ceto sun tsamo gawarwakin mutane 115 zuwa ƙarfe 5 na yammacin jiya Juma'a a Mokwa.
Mutane 12 daga gida daya sun mutu a ambaliya a Mokwa, Neja yayin da ake fargabar mutum 60 sun rasa rayuka, ciki har da almajirai 50 da ba a gano ba.
Kungiyar gwamnonin Najeriya ta nuna damuwa kan ambaliyar ruwa da aka samu a karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja. Mutane da dama sun rasu sakamakon ambaliyar
Jihar Niger
Samu kari