Gwamnan Arewa Dauki Yan Sa Kai 7,000 Aiki Don Magance Matsalar Rashin Tsaro

Gwamnan Arewa Dauki Yan Sa Kai 7,000 Aiki Don Magance Matsalar Rashin Tsaro

  • Gwamnatin Kaduna ta jaddada kokarin da take yi na tabbatar da tsaro da kawar da bata gari daga jihar
  • Gwamna Uba Sani ya dauki matasa 7,000 aiki domin kara su a cikin rundunar yan sa kai ta jihar
  • A ranar Asabar, 2 ga watan Satumba ne aka kaddamar da horar da matasan da aka zabo daga fadin hananan hukumomi 23 na jihar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta dauki matasa 7,000 aiki domin kara su cikin rundunar yan sa kai ta jihar a kokarin da take na magance matsalar rashin tsaro a jihar.

Da yake magana a yayin fara horar da sabbin yan sa kan a Kwalejin Yan Sanda da ke Kaduna, Gwamna Uba Sani ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don kakkabe annobar fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran laifuka masu halaka da ke barazana ga zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Dalibai Za Su Dara a Jihar Arewa Yayin da Gwamnansu Ke Shirin Farfado Da Tsarin Biyansu Tallafin Karatu

Uba Sani ya dauki yan sa kai 7,000 aiki a jihar Kaduna
Gwamnan Arewa Dauki Yan Sa Kai 7,000 Aiki Don Magance Matsalar Rashin Tsaro Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

An zabo dubban matasan, maza da mata da suka a kwalehin yan sandan da ke babban birnin jihar daga kananan hukumomi 23 na jihar.

Kamar yadda Channels TV ta rahoto, gwamnan ya ce za a tura yan bangar zuwa yankunan karkara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda aka zabo matasa 7,000 don aikin sa kai a Kaduna

An hada gwiwa da masu ruwa da tsaki a kananan Hukumomi, sarakunan gargajiya da shugabannin addini wajen dauka da tantance zakakuran matasan.

Gwamna Sani ya yarda cewa baya ga magance matsalar rashin tsaro da ci gaban da wannan shiri zai kawo jihar, zai kuma samawa matasa ayyukan yi.

Jaridar Aminiya ta nakalto gwamnan na cewa:

“Daga cikin manyan manufofinmu, akwai zancen kara yawan dakarun rundunar yan sa-kai (KADVS). Tun bayan kafa ta take ta fadi tashi don ganin ta yi aiki da sauran rundunonin tsaro domin dakile miyagu.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani Ya Dau Zafi Kan Kisan Masallata a Kaduna, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni

“Sai dai kuma muna fama da matsalar karancin ma’aikata. Dalili da yasa kenan gwamnatinmu ta yanke shawarar kara daukar wadannan matasa.
“Sai da muka zurfafa bincike sannan muka hada kai da Shugabannin Kananan Hukumomi da kuma masu rike da sarautun gargajiya kafin mu zakulo wadannan zakakuran matasan."

Gwamnan Kaduna ya kaddamar da bincike kan kisan masallata a Kaduna

A wani labarin, mun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, a ranar Lahadi ya bayar da umarni ga ƴan sanda da su yi bincike kan harin da aka kai a ƙauyen Saya-Saya na ƙaramar hukumar Ikara ta jihar.

Harin na ƙauyen Saya-Saya dai ya yi sanadiyyar halaka mutum bakwai ciki har da masu gudanar ibada a masallaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel