Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Farmaki 'Rukunin Gidajen El-Rufai', Sun Sace Wani Mutum

Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Farmaki 'Rukunin Gidajen El-Rufai', Sun Sace Wani Mutum

  • Masu garkuwa da mutane sun kai hari rukunin gidan El-rufai da ke yankin Bwari a babban birnin tarayya Abuja
  • Yan bindigar sun yi awon gaba da wani mazaunin yankin mai suna Chinedu bayan sun yi ta harbi a iska
  • Ciyaman na yankin Mai Baba Bego ya bayyana cewa yanzu suna zaman dar-dar ne don mutum biyar aka sace cikin yan watanni

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Mazauna yankin Kuchiko Resettlement Development Area (KRDA) da ke Bwari sun koka kan yawan sace-sacen mutane a cikin yankin.

Hakan ya biyo bayan lamarin da ya afku baya-bayan nan a safiyar Asabar, 2 ga watan Satumba, a yankin da aka fi sani da rukunin gidajen El-Rufai wato ' El-Rufai Estate'.

Yan bindiga sun sace mutane a Abuja
Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Farmaki Rukunin Gidajen El-Rufai, Sun Sace Mazauna Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Yan bindiga sun sace mazaunin Abuja

Sace-sacen mutane don karbar kudin fansa ya zama ruwan dare a yankuna da dama a Najeriya cikin yan shekarun nan.

Kara karanta wannan

Ma’aurata 7 Sun Hada Bikinsu Don Ragewa Juna Zafin Kashe Kudi, Hotunan Sun Yadu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahin tsaro na daya daga cikin batutuwan da ke gaban shugaban kasa Bola Tinubu, wanda aka rantsar a watan Mayu.

Yan bindiga sun yi awon gaba da mutumin mai suna Chinedu daga gidansa da cikin rukunin gidajen.

Matar mutumin ta yi bayanin cewa masu garkuwa da mutanen da ke dauke da muggan makamai sun tisa keyar mijinta bayan sun haura ta katanga domin samun damar shiga cikin gidan nasu.

Jaridar Daily Trust ta nakalto matar na cewa:

"Sun yi ta harbi a iska domin tsorata iyalinmu da makwabta kafin suka yi awon gaba da mijina."

Mai Baba Bego, shugaban yankin wanda ya yi magana kan lamarin, ya ce mutane biyar aka sace cikin yan watannin da suka gabata, rahoton Naija News.

Baba Bego ya ce:

"Yanzu muna rayuwa cikin tsoro don babu wanda ya san wanene zai zama mutum na gaba."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: NLC Ta Sanar Da Tsunduma Yajin Aiki Na Kwanaki 2, Ta Bayyana Dalili

Ba a samu jin ta bakin Josephine Adeh, jami'ar hulda da jama'a na rundunar yan sandan babban birnin tarayya Abuja, ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Yan bindiga sun kashe masallata a masallacin Kaduna

A wani labarin, mun ji cewa wasu da ake zaton yan bindiga ne sun farmaki masallata a wani masallaci a kauyen Saya-Saya da ke karamar hukumar Ikara ta jihar Kaduna, inda suka kashe mutum bakwai.

An bindige mutum biyar a cikin masallacin, yayin da aka tsinci gawarwakin sauran mutanen biyu a wasu wurare daban-daban a cikin yankin, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng