Manyan Labarai A Yau
Wani bidiyon mage da ta shigo masallaci ta ya hau kafar limami yayin da ya ke jan salla ya dauki hankulan mutane, wasu na ganin shaukin Kurani ya janyo magen.
Abdulmumin Jibrin ya bayyana cewa bai kamata musulmi ɗan Arewa ya zama shugaban majalisar dattawa ba. Yace duk mai son ƙasar nan ba zai so aukuwar hakan ba.
Rundunar ƴan sandan jihar Delta ta cafke wani jami'in ta bisa zargin halaka wani ɗan kasuwa. Ana zargin ɗan sandan da halaka ɗan kasuwa saboda kuɗin cin hanci.
Bankunan Najeriya na ƙara faɗaɗa harkokin kasuwancin su a nahiyar Afrika. Bankin Access yana a sahun gaba inda ya siya wasu bankuna biyar a nahiyar Afrika.
Wasu ƴan aikin gidan mutum biyu sun gurfana a gaban kotun shari'ar musuƙunci a Kano, bisa zargin sace zinaren maƙudan kuɗaɗe a gidan da aka ɗauke su suna aiki.
Zabaɓben mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya yiwa ƴan achaɓa alƙawarin cewa zai hana ƙwacewa da lalata musu babura, da ake yi a faɗin ƙasar nan..
An samu asarar a rikicin da ya ɓarke tsakanin ƴan sanda da ƴan achaɓa a jihar Legas. Wani jami'in ɗan sanda guda ɗaya ya rasa ransa a cikin rikicin da ya ɓarke.
Duk Duniya yanzu babu mai kudin kamar Bernard Arnault mai LVGH. A yau Arnault ya ba Dala biliyan 200 baya, dukiyarsa ta nunka ta Bill Gates sau biyu har da kari
Tsohon ministan sufurin jiragen sama a Najeriya, Osita Chidoka, ya yi babban rashi ranar Litinin da ta shiga, mahaifiyarsa ta rasu tana da shekaru 75 a duniya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari