Yanzu-Yanzu: Rikici Ya Barke Tsakanin 'Yan Sanda Da 'Yan Achaba, An Samu Asarar Rai

Yanzu-Yanzu: Rikici Ya Barke Tsakanin 'Yan Sanda Da 'Yan Achaba, An Samu Asarar Rai

  • Wani jami'in ɗan sanda ya rasa ran sa a rikicin da ya ɓarke tsakanin ƴan achaɓa da ƴan sanda a Legas
  • Ƴan achaɓan sun yi taho mu gama ne da jami'an ƴan sanda a tashar mota Cele kan titin Oshodi-Apapa a jihar
  • An ƙara aikewa da ƙarin jami'an tsaro zuwa inda lamarin ya auku domin kwantar da tarzomar

Jihar Legas- An halaka wani jami'in ɗan sanda ranar Laraba, a tashar motar Cele kan babban titin Oshodi-Apapa a jihar Legas, a yayin wanu rikici da ƴan Achaɓa.

Fusatattun ƴan Achaɓan sun kuma yi awon gaba bindigogi uku daga hannun jami'an ƴan sandan. Rahoton The Nation

Sanda
Yanzu-Yanzu: Rikici Ya Barke Tsakanin 'Yan Sanda Da 'Yan Achaba, An Samu Asarar Rai Hoto: The Nation
Asali: UGC

Jim kaɗan bayan an halaka jami'in ɗan sandan, ƴan achaɓan wanda yawan su yakai mutum 100 sun ɗunguma zuwa kan ƙarshen hanyar Mil 2.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana Dangane Da Badakalar Bacewar N20bn Daga Asusun NNPC

Jaridar The Nation tace ta gan su ɗauke da makamai irin su adda, wuƙaƙe, manyan sanduna da sauran makamai, sun yi kan masu tafiya a ƙasa da masu motoci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutane da dama sun ranta ana kare domin gujewa ƴan achaɓan.

An turo jerin gwanon motocin ƴan sanda domin murƙushe ƴan achaɓan.

Jami'an waɗanda suka zo a cikin motoci shida, sun kori ƴan achaɓan zuwa ƙarshen titin Mil 2.

Ku saurari ƙarin bayani......

'Yan Sanda Sun Kulle Majalisar Dokokin Jihar Plateau, Bayanai Sun Bayyana

A wani labarin na daban kuma, ƴan sanda sun kulle majalisar dokokin jihar Plateau da safiyar ranar Laraba.

Jami'an ƴan sandan sun kulle majalisar bayan an samu tashin hankali kan shugabancin majalisar, inda ɓangarori biyu basa ga maciji da juna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel