Access Bank, Fidelity Na Kan Gaba Cikin Bankunan Najeriya Da Ke Siyan Wasu Bankuna a Afrika

Access Bank, Fidelity Na Kan Gaba Cikin Bankunan Najeriya Da Ke Siyan Wasu Bankuna a Afrika

  • Access Bank yana kan gaba akan sauran bankunan Najeriya da suke siyan wasu bankuna a Afrika
  • Bankin a cikin shekara huɗu da suka gabata, ya siya kusan bankuna hudu a nahiyar Afrika yayin da yake cigaba da mamaye kasuwannin Afrika
  • Haka kuma, Fidelity Bank ya sanar da siyan Union Bank a tarayyar UK a watan Yunin shekarar 2022

A cikin shekara huɗu da suka gabata bankin Access yana cigaba da nuna yunwar sa kan siyan wasu bankuna a nahiyar Afrika da wasu ma'aikatun kuɗi a ƙasashen Afrika.

A kwanan nan, Access Holdings, uwar kamfanin ya sanya $300m a cikin bankin domin kammala siyan bankunan da yake yi a Afrika da kuma ƙara faɗaɗa ayyukanta a nahiyar.

Bankuna
Access Bank, Fidelity Na Kan Gaba Cikin Bankunan Najeriya Da Ke Siyan Wasu Bankuna a Afrika Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A cikin shekara huɗun da suka gabata, bankin ya siya fiye da bankuna uku a cikin ƙasahen Afrika uku, wanda masu sharhu suke ganin namijin ƙoƙari ne wajen mamaye kasuwar bankuna a nahiyar Afrika.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Sufetan Yan Sanda Na Ƙasa Ya Gana da Shugaban PSC, An Samu Gagarumin Ci Gaba

A shekarar 2021, Access Bank ya sanar da shirin sa na haɗe ayyukan sa waje ɗaya a ƙasar Mozambique ta hanyar siyan wani banki a ƙasar ta yankin Afrika ta Kudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Reshen bankin ya cimma yarjejeniya domin siyan African Banking Corporation, tare da taimakon kamfanin Atlas Mara Limited. Sai dai bankin bai bayyana kuɗin da ya kashe wajen siyan bankin na ƙasar Mozambique ba.

Masu sharhi sun bayyana cewa bankin yana son harkokin kasuwancin sa na wajen Najeriya su riƙa samar masa da kaso 30% na ribar da yake samu.

A cikin wannan shekarar Access Bank ya sanar da siyan kaso mafi tsoka a wani bankin ƙasar Afrika ta Kudu, Grobank. Bankin ya sauya sunan sa a hukumance zuwa Access Bank. Rahoton Premium Times

A watan Yunin 2021, Reuters ta rahoto cewa Access ya siya kaso mafi tsoka a bankin African Banking Corporation of Botswana for cash, wata ɗaya bayan siyan bankin Grobank.

Kara karanta wannan

Akwai Cash: Masu PoS Sun Ji Wuya Sun Rage Kudin Da Suka Tatsa a Hannun Mutane Yayin Da CBN Ya Sake Fitar Da Sabon Umurni

A cikin watan Janairun wannan shekarar, Bloomberg ya rahoto cewa Access Bank yana duba yiwuwar siyan Atlas Mara, cinikin da bankin ya kammala makonni kaɗan da suka wuce da siyan Zambian Bank.

Access Bank ya kuma siya bankin ƙasar Kenya, Sidian Bank kan kuɗi $36.7m a watan Yunin shekarar da ta gabata. Yarjejeniyar za ta sanya bankin samun iko kan kaso 83.4% na bankin.

Bankin ya kuma siya kaso 99.98% a bankin Kenyan Transnational Bank kan kuɗi $12.8m, sannan tuni har ya sauya sunan sa zuwa Access Bank.

Fidelity Bank ya siya Union Bank a tarayyar UK

A watan Yunin 2022, Fidelity Bank ya bayyana cewa ya shiga yarjejeniyar siyan kaso 100% a bankin Union Bank a UK.

Hakan na zuwa ne bayan bankin Titan Trust Bank ya siya Union Bank na Najeriya.

Masu PoS Sun Zaftare Kudin Da Suke Amsa Yayin Da Aka Samu Wadatuwar Kudi

Kara karanta wannan

Sanatan APC Ya Fasa Kwai, Ya Bayyana Kulla-Kular Da 'Yan Siyasa Ke Yi Domin Samun Shugabancin Majalisa

A wani labarin na daban kuma, kasuwar masu PoS ta fara ja da baya yayin da ake samun wadatuwar kuɗaɗe a yanzu.

Hakan ya sanya su dole zaftare kaso mai yawa na kuɗaɗen da suke caja idan aka cira kuɗi a wajen su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel