Manyan Labarai A Yau
Kotun zabe ta tsige Chijioke Okereke na jam’iyyar LP. Har zuwa lokacin tsige shi, Okereke ya kasance dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Aninri.
Al'ummar Yarbawa mazauna Kano sun gudanar da taron addu'a ta musamman don neman Allah ya yi wa jagoran Kwankwasiyya, Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso jagoranci.
Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ta cafke tare da titsiye mataimakiyar gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Aisha Ahmad, kan badaƙalar $300m.
Sarkin Birnin Gwari, Malam Zubairu Jibril, Maigwari II ya amince da musanya wasu hakimai biyu daga cikin kokarin da yake yi na inganta lamarin tsaro a masarautarsa.
Miinistan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa ya gayyato EFCC da ICPC su binciki magabacinsa Muhammad Bello.
Wata mata yar Najeriya wacce ta shafe tsawon shekaru 10 tana aiki a matsayin mai reno ta samu kyautar gida daga uwar dakinta a matsayin tukwicin godiya.
Ayarin motocin matar gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Aisha Bala Muhammad, sun makale a wani hanya mara kyau, a hanayarta ta zuwa kaddamar da wani cibiyar lafiya.
Gwamnan jihar Ribas Fubara ya ayyana neman wani mai suna Gift David Okpara Okpolowu, wanda aka fi sani da 2-Baba da yan kungiyarsa kan kisan DPO Bako Angbashim.
Wani bature ya samu abubuwa da yawa bayan ya canja dalarsa zuwa naira. Yan kasar waje sun cika da mamakin dalilin da yasa abubuwa ke da sauki a Najeriya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari